'Yan bindiga sun tare matafiya, sun yi garkuwa da 20 daga ciki a Katsina

'Yan bindiga sun tare matafiya, sun yi garkuwa da 20 daga ciki a Katsina

- 'Yan bindiga sun tare matafiya a kan babbar hanyar Jibia zuwa Gurbi ta jihar Katsina inda suka sace matafiya

- Kamar yadda kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina ya sanar, ya ce motarsu ce ta lalace a kan hanya har 'yan bindigar suka samesu

- Duk da direban ya ce matafiya 20 'yan bindigar suka sace, rundunar 'yan sanda ta ce tara ne kuma sun ceto biyu daga ciki

Wasu 'yan bindiga sun kwashe wasu matafiya da ke kan babbar hanyar Jibia zuwa Gurbi ta jihar Katsina, inda suka yi awon gaba da su zuwa inda babu wanda ya sani.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta gano, a yayin da suke kan hanyar shiga daji da matafiyan, direban yayi yunkuri tserewa inda a take suka harbeshi suka bar shi a nan.

Majiyar ta kara da cewa, wasu mazauna kauyen ne suka tsinci direban bayan kwanaki biyu da aukuwar lamarin.

A nan ya sanar da jama'ar cewa, a kalla mutu 20 'yan bindigar suka yi garkuwa da su. A halin yanzu yana asbiti inda yake karbar taimakon likitoci.

A lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da aukuwar lamarin amma yace mutum tara kacal aka sace.

Ya ce sun ceto mutum biyu daga cikin wadanda aka sace.

"Motarsu ce ta lalace shine suka tsaya gyara a daji. A hakan 'yan bindigar suka kama su. Kafin zuwan 'yan sanda, tuni sojoji suka isa," SP Isah yace.

Ya kara da cewa ana binciken lamarin a halin yanzu.

KU KARANTA: Da duminsa: Najeriya ta tabbata cibiyar mutuwar yara masu kasa da shekaru 5 a duniya

'Yan bindiga sun damke tare matafiya, sun yi garkuwa da wasu a Katsina
'Yan bindiga sun damke tare matafiya, sun yi garkuwa da wasu a Katsina. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Suna shan wiwi saboda su fatattaki miyagun aljanu - Lauya ya kare matasa 3 a kotu

A wani labari na daban, mazauna jihar Zamfara sun yi kuma yadda lamarin rashin tsaro ya koma kauyuka da garuruwan karamar hukumar Nahuce a jihar.

HumAngle ta ruwaito cewa labarin da ta samu daga majiya a Nahuce cewa yan ta'adda sun koma kauyukan kuma suna cin karansu ba babbaka.

A ranar Litinin, 7 ga Satumba, yan ta'adda sun kai hari garin Yar Kaita da Garka a Nahuce inda suka kashe mutum daya, suka yi awon gaba da matasa uku bayan jikkata mutane da yawa.

A Jawabin hirar waya da HumAngle ta samu, yan ta'addan sun bukaci milyan 100 kudin fansa kafin su sakesu. Mutanen garin Nahuce sun ce yan bindigan na kai hari ne tsakiyar dare.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel