'Yan sanda sun kama kayan tallafin korona na jihar Benue da aka sayar a kasuwar Kano

'Yan sanda sun kama kayan tallafin korona na jihar Benue da aka sayar a kasuwar Kano

- An kama katon din talliyar indomie masu yawa wadanda aka karkatar daga jihar Benue aka sayar a kasuwar Singer ta Kano

- Yan sandan da suka kama kayayyakin sun ce kiyasin kudin taliyar katon 1,958 ya kai N4,411,800

- Kwamishinan yan sanda na jihar Kano, Habu Sani ne ya sanar da hakan yayin da ya ke gabatar da wasu da ake zargi da aikata laifuka a jihar

A ƙalla katon ɗin taliya indomie guda 1,958 cikin 3,850 da ya kamata a raba wa mutane a matsayin tallafi a jihar Benue ne yan sanda suka gano an sayar da su a Kano.

Yan sanda sun yi nasarar kama wadanda ke da hannu wurin karkatar da kayan tallafin, an kuma yi holen su tare da wasu da ake zargi da aikata wasu laifukan a ofishin ƴan sanda ta Bompai.

'Yan sanda sun kama kayan tallafin korona na jihar Benue da aka sayar a kasuwar Kano
'Yan sanda sun kama kayan tallafin korona na jihar Benue da aka sayar a kasuwar Kano. Hoto daga The Punch
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Garba Shehu: An sayar da man fetur N600 kowanne lita a mulkin PDP

Wasu daga cikin wadanda aka yi holen su sun hada da wadanda ake zargi da garkuwa da mutane, damfara, satar mota, safarar miyagun kwayoyi da sauran su.

An ƙiyasta cewa kuɗin talliyar da aka karkatar mai laƙabain "CA-COVID-19" ya kai Naira miliyan 4,411,800.

An gano talliyar ne a fitaccen kasuwar Singer da ke Kano kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Da ya ke yi wa manema labarai jawabi a hedkwatar ƴan sanda, kwamishinan ƴan sanda na jihar, Habu Sani an yi nasarar kama masu laifin ne sakamakon jajircewar yan sandan Puff Adder da wasu sabbin dabarun yaki da masu laifuka.

KU KARANTA: Masu garkuwa sun sace yaran ma'aji a Zamfara su uku, sun kuma kashe maƙwabcinsa

A cewar kwamishinan, rundunar ta Puff Adder suna cigaba da ayyukansu ne bisa umurnin da Sufeta Janar na ƴan sanda ya bayar na kawar da miyagu.

Ya kuma ce rundunar ta yi nasarar kama mutane fiye da 259 a cikin makonni shida da suka wuce da ake zargi da aikata laifuka daban-daban.

A wani rahoton da Legit.ng ta wallafa kun ji cewa gwamnatin jihar Abia ta ce ta gano bullar cutar tarin tuberculosis (TB) na shanu a jihar hakan yasa ta gargadi mazauna jihar su dena cin huhun shanu.

Kwamishinan noma na jihar, Ikechi Mgboji ne ya sanar da hakan a ranar Talata 8 ga watan Satumba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel