Masu garkuwa sun sace yaran ma'aji a Zamfara su uku, sun kuma kashe maƙwabcinsa

Masu garkuwa sun sace yaran ma'aji a Zamfara su uku, sun kuma kashe maƙwabcinsa

- Wasu masu garkuwa sun kai hari garin Nahuche da ke karamar hukumar Bungudu a Zamfara sun sace yaran ma'aji a jihar

- Yan bindigan da aka ce sun taho a babura sun kuma bindige wani mutum mai suna Malam Kamalu Nahuche har lahira

- Bayan yaran ma'ajin uku da suka sace, yan bidigan sun kuma shiga gidan wani ɗan kasuwa sun saci kuɗi sun kuma tafi da yaransa

Wasu masu garkuwa da mutane da ake kyautata zaton yan bindiga ne sun sace yaran ma'aji a jihar Zamfara, Alhaji Yusuf Marafa kuma sun kashe makwabcinsa.

Maharan sun kai harin ne a gidansa da ke garin Nahuche a ƙaramar hukumar Bungudu na jihar kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Masu garkuwa sun sace yaran ma'aji Zamfara su uku, sun kuma kashe maƙwabcinsa
Masu garkuwa sun sace yaran ma'aji Zamfara su uku, sun kuma kashe maƙwabcinsa
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Bidiyo: Amarya ta fasa auren mijinta a lokacin da aka tafi wurin daurin aure

A cewar wata majiya, yaran da aka sace sune Mansur Yusuf, Sa'adu Yusuf da Anas Yusuf yayin da makwabcinsa da suka bindige har lahira kuma sunansa Malam Kamalu Nahuche.

Wani mazaunin garin da ya ce sunansa Alhaji Dahiru ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa masu garkuwar sun zo ne a kan babura suka wuce gidan ma'ajin suka sace yaran.

Rahotanni sun ce ƴan bindigan sun harbe makwabcinsa ne a lokacin da ya fito daga gidansa.

Dahiru ya kuma ce yan bindigan sun shiga gidan wani ɗan kasuwa, Ibrahim Maishago da niyyar shima su sace yaransa.

"Sun samu kudade da ba a tabbatar da adadin su ba a gidan sannan suka tafi da kudaden da yaran."

KU KARANTA: Mai gyaran famfo ya kashe wata mata saboda ta nemi rangwamen kuɗin aiki

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Muhammad Shehu ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce jami'an su sun tafi unguwar domin tabbatar da komi ya dawo dai-dai.

Ya kuma tabbatar wa mazauna unguwar cewa jami'an tsaro za su yi iya ƙoƙarin su domin ganin an samu tsaro da zaman lafiya a unguwar da ma jihar baki daya.

Ya bukaci mutane su cigaba da bin doka da oda su kuma zauna lafiya domin hakan zai taimaka wa ƙoƙarin da hukumomin tsaro ke yi a jihar ta Zamfara.

A wani labarin daban, kun ji cewa Hukumar kashe Gobara ta Jihar Kano ta ce wani yaro dan shekara bakwai, Umar Ado ya mutu a cikin rijiya a Unguwa Uku by Yarabawa Street a karamar hukumar Tarauni na jihar.

Sanarwar ta fito ne daga bakin mai magana da yawun hukumar, Alhaji Saidu Mohammed a ranar Laraban wannan makon kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel