Bidiyo: Ina son kasancewa da shi har abada - Mahaifiya mai soyayya da danta

Bidiyo: Ina son kasancewa da shi har abada - Mahaifiya mai soyayya da danta

- Wata mahaifiyar matashi mai shekaru 19 ta janyo cece-kuce sakamakon babban hukuncin da ta yanke wa rayuwarsu

- Matar mai suna Carlos ta bayyana a wani faifan bidiyo inda ta bayyana dalilinta na soyayya da dan cikinta

- Ta ce bata son rabuwa da shi kwata-kwata kuma tana fatan su dawwama a tare da shi har abada

Wata mahaifiya da ke soyayya da dan ta mai shekaru 19 mai suna Carlos, ta yi magana sakamakon caccakarta da ake faman yi bayan bayyanawa jama'a halin da suke ciki da tayi.

Da farko dai, ta ce bayan samun kanta da tayi cikin halin soyayyar dan cikinta, ta kira shi wata rana inda ta sanar da shi abinda take ji game da shi.

"Ka yi hakuri, ban san yadda za ka yi martani a kan wannan abun ba. Ni mahaifiyarka ce kuma kai da na ne. Ina kaunarka," ta sanar da danta.

A martanin danta, ya ce, "Na ji tsoron fada mata cewa nima ina kaunarta".

Ta ce dukkansu sun sakankance cewa ba za su iya rayuwa ba, ba tare da junansu ba saboda tsananin soyayyar da suke wa kansu, jaridar The Nation ta wallafa.

Hakazalika, bata taba jin wani abu daban ba duk da ta san da danta take soyayya. Ta ce hakan na daga cikin abinda ya faru da ita da ba za ta taba mantawa da shi ba.

KU KARANTA: Malami ya sanar da abinda zai yi idan aka gayyacesa shaida a gaban kwamitin binciken Magu

Bidiyo: Ina son kasancewa da shi har abada - Mahaifiya mai soyayya da danta
Bidiyo: Ina son kasancewa da shi har abada - Mahaifiya mai soyayya da danta. Hoto daga The Nation
Source: Twitter

KU KARANTA: Gwamnan APC da sojin Najeriya sun yi musayar kalamai, sun yi wa juna kaca-kaca

A wani labari na daban, wata uwa, uwargida Veronica Iorshe, mai shekaru 47, da ke zaune a garin Ugee, karamar hukumar Gwer, a jihar Benuwe, ta bayyana yadda ta dinga kwanciya da dan cikinta har ta kai ya yi mata ciki.

A cewar Veronica, "ni ba lalatacciyar mace ba ce. Ni mace ce dake son mijinta saboda bana son rabuwa da shi.

"Na aikata hakan ne don na kubutar da aure na, amma na kan ji nauyin abin da na aikata wasu lokutan. Na san da nauyi, amma da gaske ne na kwanta da dan cikina. Na yi hakan ne don na haifa wa mijina da. Amma sabanin yin hakan ya kubutar da aurena, sai gashi ya lalata shi."

Veronica ta ce ta yanke shawarar fara kwanciya da dan cikinta mai shekaru 20 bayan ta shafe shekaru takwas ba tare da samun haihuwa tare da sabon mijinta ba. Ta bayyana cewa batun rashin samun haihuwar yasa surukarta ta fara tsangwamarta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel