An gargadi ƴan Abia game da cin huhun sa

An gargadi ƴan Abia game da cin huhun sa

- Gwamnatin jihar Abia ta gargadi al'ummar jihar da masu cin nama su dakatar da cin huhun shanu

- Hakan na zuwa ne bayan da ma'aikatar lafiya ta jihar ta gano bullar cutar tarin TB na shanu a jihar

- Gwamnatin ta ce mutane na iya amfani da sauran tsokar da ke jikin shanu amma banda huhun domin ba a iya gane mai cutar sai anyi gwaji

Gwamnatin jihar Abia ta ce ta gano bullar cutar tarin tuberculosis (TB) na shanu a jihar hakan yasa ta gargadi mazauna jihar su dena cin huhun shanu.

Kwamishinan noma na jihar, Ikechi Mgboji ne ya sanar da hakan a ranar Talata 8 ga watan Satumba.

An gargadi ƴan Abia game da cin huhun sa
An gargadi ƴan Abia game da cin huhun sa. Hoto daga The Punch
Source: Twitter

KU KARANTA: Garba Shehu: An sayar da man fetur N600 kowanne lita a mulkin PDP

Mgboji ya ce dena cin huhun shanu zai kare mazauna jihar daga kamuwa daga cutar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

A cewarsa, cutar na janyo mutuwar jiki da rashin lafiya tare da tari kuma daga bisani mutum na iya mutuwa.

Mgboji ya ce, "Ɗaya daga cikin aikin mu shine duba duk wani shanu da za a yanka a jihar domin likitoci su tabbatar ba ya dauke da wata cuta.

DUBA WANNAN: Kwamishina ya yi murabus kwanaki 10 kafin zaɓe a Edo

"Kimanin makonni biyu da suka wuce an yanka wasu shanu biyu kuma an gano sun kamu da cutar tarin TB ta shanu. Babu yadda za a gane dabba na ɗauke da cutar sai dai idan an yanka ko anyi gwaji.

"Saboda haka muke janyo hankalin mutane da ke cin nama su dena cin huhun shanu a halin yanzu. Amma suna iya cin sauran tsokan da ke jikin shanun."

A wani labarin daban, kun ji wata babban kotu da ke zamanta a Kasuwan Nama a Jos, ranar Alhamis ta yanke wa wani mai tireda hukuncin zaman gidan yari saboda satar karas.

Kotun ta yanke wa Abba Arando mai shekaru 25 hukuncin ɗaurin shekaru biyu ne saboda samunsa da laifin satar karas da kudinsu ya kai Naira 65,000.

Alƙalin kotun, Lawal Suleiman ya yanke wa Arando hukuncin ne bayan ya amsa aikata laifin kutse, makirci da sata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel