An yanke wa mai tireda hukunci ɗaurin shekaru biyu saboda satar karas na N65,000

An yanke wa mai tireda hukunci ɗaurin shekaru biyu saboda satar karas na N65,000

Wata babban kotu da ke zamanta a Kasuwan Nama a Jos, ranar Alhamis ta yanke wa wani mai tireda hukuncin zaman gidan yari saboda satar karas.

Kotun ta yanke wa Abba Arando mai shekaru 25 hukuncin ɗaurin shekaru biyu ne saboda samunsa da laifin satar karas da kudinsu ya kai Naira 65,000.

Alƙalin kotun, Lawal Suleiman ya yanke wa Arando hukuncin ne bayan ya amsa aikata laifin kutse, makirci da sata.

An yanke wa mai treda hukunci ɗaurin shekaru biyu saboda satar karas na N65,000
An yanke wa mai treda hukunci ɗaurin shekaru biyu saboda satar karas na N65,000. Hoto daga Vanguard
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Bidiyo: Amarya ta fasa auren mijinta a lokacin da aka tafi wurin daurin aure

Sai dai alƙalin ya bawa wanda aka yanke wa hukuncin zaɓin biyan tara ta Naira 20,000.

Alƙalin ya shawarci wanda aka yanke wa laifin ya canja daɓi'unsa ya dena aikata laifuka.

Tunda farko, mai shigar da ƙara, Sufeta Ibrahim Gokwat ya shaida wa kotu cewa wani Ahamad Mohammed ne ya shigar da rahoto kan satar a ofishin ƴan sanda na Laranto a ranar 5 ga watan Satumba.

Gokwat ya ce wanda aka yanke wa hukuncin ya amsa cewa ya shiga gonar wanda ya yi karar ya girbe karas da kudinsu ya kai N65,000 ba tare da izinin mai gonar ba.

KU KARANTA: Fittacen fasto na ƙasar Ghana ya bindige matarsa har lahira a Amurka

Laifin ya ci karo da sashi na 327, 312 da 271 na dokar Penal Code.

A wani rahoton daban, kun ji cewa wata mata ta zame ta faɗa cikin dam a lokacin da ta ke ɗaukan hotuna yayin wata liyafar cin abinci na masoya da aka yi a Chepkiit Waterfalls da ke yankin Nandi.

Ruwa ya yi awon gaba da Dorcas Jepkemoi Chumba mai shekaru 31 a ranar Lahadi yayin da saurayinta Banjamin Kazungu ke amfani da wayan ta yana ɗaukan ta hoto.

Iyalan Miss Chumba da suka fito daga kauyen Kapchorwa a Keiyo ta Kudu sun tare a Chepkiit Waterfalls tun ranar Lahadi da nufin za a gano gawarta.

Masunta a yankin da ke neman gawar ta ba suyi nasara ba a lokacin da ake haɗa wannan rahoton kamar yadda da Nation ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel