Yajin aiki: Likitoci da FG sun saka hannu a kan sabuwar yarjejeniya

Yajin aiki: Likitoci da FG sun saka hannu a kan sabuwar yarjejeniya

Gwamnatin tarayya da shugabannin kungiyar likitoci masu neman kwarewa (NARD), a daren jiya sun saka hannu a kan sabuwar yarjejeniyar fahimta domin shawo kan matsalar yajin aikin da likitocin suka fara.

Bayan saka hannu a kan yarjejeniyar, shugabannin NARD ana tsammanin za su hadu a yau Alhamis domin duba yuwuwar janye yajin aikin.

An sa hannu a takardar yarjejeniyar bayan taron sasancin da ya samu halartar ministan kwadago da aikin yi, Sanata Dr Chris Ngige, shugabannin NARD da na NMA, ma'aikatar lafiya ta tarayya, ma'aikatar kudi, kasafi da tallafi da kuma ofishin akanta janar na tarayya.

A yayin jawabi ga manema labarai bayan taron sasancin, ministan kwadago, Dr Chris Ngige, ya ce a halin yanzu asibitocin tarayya sun mallaki isassun kayayyakin kariya domin amfanin likitocin.

KU KARANTA: Karin farashin man fetur: Jama'ar Kaduna sun koka da ninkuwar kudin mota

Yajin aiki: Likitoci da FG sun saka hannu a kan sabuwar yarjejeniya
Yajin aiki: Likitoci da FG sun saka hannu a kan sabuwar yarjejeniya. Hoto daga Vanguard
Asali: Getty Images

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, daga cikin wasu cigaba da aka samu, ya ce: "Gwamnatin tarayya ta biya N9.3 biliyan ga kamfanonin inshora da kuma biyan hakkokin ma'aikatan lafiya da suka rasu."

KU KARANTA: Malami ya sanar da abinda zai yi idan aka gayyacesa shaida a gaban kwamitin binciken Magu

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya ta umarci shugabanni asibitoci na tarayya da su gaggauta fara amfani da manyan likitoci da kuma masu hidimar kasa domin maye gurbin likitocin da suka tafi yajin aiki.

Ministan lafiya, Dr Osagie Ehanire, ya bada wannan umarnin a wata takarda da ya fitar a garin Abuja a ranar Laraba, jaridar The Punch ta wallafa.

Yana yin martani ne game da yajin aikin da kungiyar likitoci masu neman kwarewa suka yi a kan rashin biyansu alawus na hatsarin Covid-19 da sauran bukatunsu.

Ya ce, "Cike da matukar damuwa nake duba yajin aikin da kungiyar likitoci masu neman kwarewa suka fada a ranar Talata, 7 ga watan Satumban 2020.

"Dole ne mu tuna cewa, babban aikin likitoci da dukkan masana kiwon lafiya shine ceton rai. Fara yajin aiki a wannan lokacin da kasar da duniya ke fuskantar annoba bai dace ba.

"Ma'aikatar lafiya ta tarayya don haka ta gane cewa ya zama dole ta samo dabarun da za su hana jama'a fuskantar kalubalen yajin aikin.

"Tana kira ga dukkan shugabannin ma'aikatun lafiya na tarayya da su cigaba da tabbatar da kiyaye dokokin dakile yaduwar cutar korona da aka aike musu.

“A gaggauta ci gaba da ganin marasa lafiya. Kwararrun likitoci da likitoci masu hidimtawa kasa su ci gaba da aiki."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel