Mai gyaran famfo ya kashe wata mata saboda ta nemi rangwamen kuɗin aiki

Mai gyaran famfo ya kashe wata mata saboda ta nemi rangwamen kuɗin aiki

Wani mai gyaran famfo a Kazakhstan ya kashe wata kwastomarsa bayan ta nemi ya yi mata rangwamen kuɗin aiki.

Ya kuma yi wa mahaifiyarta da makwabciyarta rauni daga bisani kamar yadda LIB ya ruwaito.

Mutumin ya mai shekaru 43 da ba a bayyana sunansa ba ya caka wa Inna Murzaeva mai shekaru 32 wuka ta mutu nan take.

Mai gyaran famfo ya kashe wata mata saboda ta nemi rangwamen kuɗin aiki
Mai gyaran famfo ya kashe wata mata saboda ta nemi rangwamen kuɗin aiki
Source: Facebook

Ya kuma yi wa mahaifiyarta da makwabcinta na miji rauni a lokacin da suka yi ƙoƙarin ceton ta.

Inna ta mutu nan take yayin da mahaifiyar ta da makwabcinta suna asibiti rai a hannun Allah yayin da shi kuma an kama shi.

Lamarin mai ban tsoro ya faru ne a ranar 4 ga watan Satumba a birnin Almaty da ke arewa maso gabashin kasar.

A cewar rahotonni, Inna ta gayyaci mai gyaran famfon zuwa gidanta ne bayan ta gan shi a yanar gizo.

DUBA WANNAN: Boko Haram ta kashe mutum huɗu yayin da suke barci, ta ƙona wasu uku da ransu a Borno

Sun fara cacar baki ne kawai domin Inna ta nemi ya yi rangwame kan kudin aikinsa.

Cacar bakin ya yi zafi kawai sai mai gyaran famfon ya ciro wuƙa daga aljihunsa ya kai wa Inna da mahaifiyar ta mai shekaru 63 hari a cewar rahotonni.

Mai gyaran famfo ya kashe wata mata saboda ta nemi rangwamen kuɗin aiki
Mai gyaran famfo ya kashe wata mata saboda ta nemi rangwamen kuɗin aiki
Source: Facebook

Ihun matan ya janyo hankulin wani mutum da ke gidan da ke makwabtaka da su ya zo kawo musu ɗauki amma shima ya jikkata.

Mutumin ya tsere cikin hanzari amma wani shaida ganin ido ya gan shi.

Shaidan ya shaida wa kafar watsa labarai na ƙasar, "Mutumin na rike da makami mai kama da wuka da aiki a gida da jini da ɗiga daga jikinsa. Mun kira ƴan sanda da motar asibiti."

Inna ta mutu sakamakon munannan raunin da ya yi mata kafin motar asibiti ya iso inji masu bincike.

Mai gyaran famfo ya kashe wata mata saboda ta nemi rangwamen kuɗin aiki
Mai gyaran famfo ya kashe wata mata saboda ta nemi rangwamen kuɗin aiki
Source: Facebook

Ƙawar Inna Oksana Feller ta ce: "Ya yanka maƙwogoron ta saboda haka babu yadda za ta yi rai."

Sauran mutane biyun kuma an garzaya da su asibiti cikin gaggawa.

KU KARANTA: Ba da mugun nufi na yi zanen barkwancin auren Hanan ba - Bulama

Shaidun da suka ga mutumin sun bawa yan sanda kwatancensa kuma aka kamo shi aka tsare shi.

Yayin da ake masa tambayoyi, wanda ake zargin ya ce, "Na yi amfani da wukar na caka mata a jiki, wannan shine karo na farko da na ke kai wa mace hari."

Shugaban ƴan sanda na riko, Tanat Nazanov ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce, "wanda ake zargin ya kai wa matar hari a lokacin da suka cinikin kuɗin aikinsa.

"Ana tuhumarsa da kisa kuma an tsare shi. Akwai yiwuwar za a masa ɗaurin shekaru 15 idan aka tabbatar da laifinsa."

A wani labarin daban, kun ji yan Sanda da ke birnin tarayya Abuja sun kama wani mutum da ya saci mota mallakin hukumar kiyayye haɗɗura ta ƙasa, FRSC, daga hedkwatar hukumar da ke Wuse Zone 5, Abuja.

Sanarwar da mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Abuja, DSP Anjuguri Manzah ya fitar ta ce an kama Hamisu Tukur mai shekaru 25 ne yayin bincike da hukumar ke yi a titi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel