Matashi ya kashe mahaifiyarsa a kan ruwan lemo da kuma motarta

Matashi ya kashe mahaifiyarsa a kan ruwan lemo da kuma motarta

Matashi mai shekaru 29 ya kashe mahaifiyarsa har lahira sakamakon rikicin da suka yi a kan ruwan lemo da amfani da motarta wurin neman aiki, 'yan sanda suka ce.

Kamar yadda Koaa.com ta wallafa, Luis Pages, ya sanar da masu bincike cewa ya rasa tunaninsa yayin rikici da mahaifiyarsa mai shekaru 59.

Sunan dattijuwar Miriam Gonzalez, kuma tana zama a yankin arewacin gabar tekun Miami. Dan ta ya harbeta sau babu adadi.

Pages da kansa ya kira 911 bayan ya gama harbin inda ya sanar da su cewa ya harbe mahaifiyarsa, wani dan sanda yace.

A yayin da dan sanda ya isa gidan wurin karfe 5 na yamma, Pages ya sanar da shi cewa "na kashe mahaifiyata, ku kaini gidan yari", rahoton yace.

An damke Pages inda aka kaishi ofishin 'yan sanda domin amsa tambayoyi. Ya sanar da masu tuhumarsa cewa, mahaifiyarsa ta dauka wuka inda ta yi barazanar kashesa.

A wannan lokacin ya dauka bindiga inda ya dinga harbinta har ta mutu, rahoton 'yan sandan ya sanar.

Ya sanarda masu bincike cewa, ya yi kokarin kashe kansa, amma sai ya gane cewa harsasansa sun kare. Daga nan ya kira 911.

Pages yana garkame yanzu kuma a halin yanzu bashi da lauyan kansa, jaridar The Punch ta wallafa.

KU KARANTA: Hotuna: Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 14 a Zamfara, ta kwashe gada a Sokoto

Matashi ya kashe mahaifiyarsa a kan ruwan lemo da kuma motarta
Matashi ya kashe mahaifiyarsa a kan ruwan lemo da kuma motarta. Hoto daga The Punch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Malami ya sanar da abinda zai yi idan aka gayyacesa shaida a gaban kwamitin binciken Magu

A wani labari na daban, wata babbar kotu a jihar Zamfara ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan wani mutum da ya kashe mahaifiyarsa da yan uwansa mata biyu.

An gurfanar da Kamal Yusuf da wasu mutane biyu —Armayau Shehu da Caleb Humphrey a gaban kotu bisa zarginsu da aikata laifuka uku amma Humphrey ya mutu a gidan yari kafin a kammala sharia.

Laifukan da ake tuhumarsu da aikatawa sun hada da hadin baki, fashi da makami da kisa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Da ya ke zartar da hukuncin, babban alkalin jihar, Mai sharia Kulu Aliyu ta yanke wa Kamal Yusuf hukuncin kisa ta hanyar rayata yayin da shi kuma mutum na biyu da ake tuhuma, Armayau Shehu an wanke shi an kuma sake shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel