Yan bindiga sun sake komawa jihar Zamfara

Yan bindiga sun sake komawa jihar Zamfara

Mazauna jihar Zamfara sun yi kuma yadda lamarin rashin tsaro ya koma kauyuka da garuruwan karamar hukumar Nahuce a jihar.

HumAngle ta ruwaito cewa labarin da ta samu daga majiya a Nahuce cewa yan ta'adda sun koma kauyukan kuma suna cin karansu ba babbaka.

A ranar Litinin, 7 ga Satumba, yan ta'adda sun kai hari garin Yar Kaita da Garka a Nahuce inda suka kashe mutum daya, suka yi awon gaba da matasa uku bayan jikkata mutane da yawa.

A Jawabin hirar waya da HumAngle ta samu, yan ta'addan sun bukaci milyan 100 kudin fansa kafin su sakesu.

Mutanen garin Nahuce sun ce yan bindigan na kai hari ne tsakiyar dare.

A ranar 11 ga Satumba 2018, yan bindiga suka kai harin farko yankin Sabon Gari na karamar hukumar inda suka far wa Alhaji Ibrahim Sanko.

Sun koma garin Yar Kaita inda suka kaiwa Alhaji Yusuf Na'abu a ranar 22 ga yuli, 2020.

Bayan haka kuma a ranar 6 ga Agusta, 2020, sun kuma kai hari gidan Alhaji Badamasi Nahutawa Petroleum a Sabon Gari.

Har yanzu yan bindigan basu daina kai hari jihar Zamfara ba duk da kokarin da gwamnatin jihar keyi.

KU KARANTA WANNAN: Duk masu ihun 'Sai Baba' har yanzu munafukai ne, ko Buhari bai iya zuwa Katsina - Sheik Bello Sokoto

Yan bindiga sun sake komawa jihar Zamfara
Yan bindiga sun sake komawa jihar Zamfara
Asali: Twitter

A wani labarin daban, Wani shahrarren malamin addinin Musulunci, Sheikh Murtala Bello Sokoto, ya caccaki shugaba Muhammadu Buhari kan matsalar rashin tsaro da ya addabi Najeriya da kuma halin kunci da wuyan da gwamnatinsa ta jefa yan Najeriya.

Sheikh Sokoto a faifan bidiyo da jaridar SaharaReporters ta gani yana mai cewa yan bindiga suna cin karansu ba babbaka a garuruwa.

DUBA WANNAN LABARIN: Jama'a sun suburbudi jami'in FRSC da ya ja hadari yayin kokarin kama mai laifi (Bidiyo)

Ya ce idan Buhari ya ki kawo sauyi da gyara, shi da al'ummarsa za suyi addu'a Allah ya kawar da shi.

Shehin Malamin ya caccaki masu yabon Buhari har yanzu inda yace munafukai ne saboda ku shi Buharin ya kasa zuwa mahaifarsa jihar Katsina sakamakon rashin tsaro.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel