Suna shan wiwi saboda su fatattaki miyagun aljanu - Lauya ya kare matasa 3 a kotu

Suna shan wiwi saboda su fatattaki miyagun aljanu - Lauya ya kare matasa 3 a kotu

Wani lauya mai kare wasu samari uku da ake zargi da shan wiwi, Tunbosun Oladipupo, a ranar Laraba ya sanar da alkali J. Omisade na wata kotun majistare da ke osogbo a jihar Osun cewa, wadanda yake karewa suna shan wiwi domin korar miyagun aljanu.

Ya bayyana cewa, duba da yanayin aikinsu, dole ne su yi amfani da wiwi domin samun kuzarin da zai basu damar yin ayyukansu.

Daya daga cikin wadanda ake karewa mai suna Samson Lucas yayin amsa tambayoyi, ya ce wiwi ta fi musu aiki fiye da taba sigari.

Wadanda ake karewa, Samson Lucas mai shekaru 25, Ayo Olamide mai shekaru 25 da Olalekan Omoniyi mai shekaru 22, an gurfanar da su a gaban kotu bayan kama su da aka yi suna shan wiwi.

An gurfanar da su sakamakon zarginsu da ake yi da mallakar layu da kuma yunkurin fashi da makami.

KU KARANTA: Bidiyo: Cristiano Ronaldo ya sake barin wani sabon tarihi a duniya, yayin da ya zama dan wasa na biyu a duniya da ya zura kwallaye 100

Suna shan wiwi saboda su fatattaki miyagun aljanu - Lauya ya kare matasa 3 a kotu
Suna shan wiwi saboda su fatattaki miyagun aljanu - Lauya ya kare matasa 3 a kotu. Hoto daga Vanguard
Asali: Twitter

KU KARANTA: Za'a yiwa daliban jihar Ogun karin aji kai tsaye ba tare da sun zana jarrabawa ba idan suka koma makaranta a ranar 21 ga watan Satumba - Dapo

Wadanda ake karewan sun ki amsa laifuka hudu da ake zarginsu da shi na mallakar laya, wiwi, makamai da kuma yunkurin fashi da makami.

Hakan ya ci karo da sashi na 516, kuma abun hukuntawa ne a sashi na 509 na dokokin laifukan jihar Osun na 2002.

Dan sanda mai gabatar da kara, Sifeta Elisha Olusegun, ya sanar da kotu cewa wadanda ke kare kansu sun aikata laifin a ranar 3 ga watan Satumban 2020 wurin karfe 1:00 na dare a yankin Orile-Owu da ke jihar Osun.

Alkalin kotun, Omisade, ya bada belin wadanda ake zargin a kan N300,000 kowannensu tare da tsayyaye daya kowanne.

Ya kara da cewa, dole tsayayyen ya kasance dan uwan wadanda ake zargin. Ya mayar da karar zuwa kotun majistare da ke Gbongan domin ci gaba da saurare a ranar 8 ga watan Okotoban 2020.

A wani labari na daban, wata matar aure mai suna Ladidi Abbas, a ranar Talata ta maka mijinta mai suna Shehu Abbas a gaban wata kotun shari'ar Musulunci da ke zama a Magajin Gari, a Kaduna.

Ladidi ta bukaci mijinta da ya sauwake mata igiyoyin aurensa, saboda dukan da take sha a hannunsa a duk lokacin da suka samu matsala, jaridar The Nation ta wallafa.

Kamar yadda tace, an kwantar da ita a asibiti na tsawon kwanaki 13 a wancan dukan da yayi mata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel