Tashin kudin Wuta da Mai: Atiku munafikin mutum ne - Jam'iyyar APC

Tashin kudin Wuta da Mai: Atiku munafikin mutum ne - Jam'iyyar APC

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta siffanta sukan da jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) da dan takarar shugaban kasarta a zaben 2019, Atiku Abubakar, kan tashin kudin man fetur a matsayin kololuwar munafinci.

Jam'iyyar ta kara da cewa babatun da Atiku ke yi ya nuna cewa munafiki ne kuma ya bayyana shi matsayin "mutum mara gaskiya kuma wanda bai cancanci a taba yarda da shi ba."

Mataimakin kakakin jam'iyyar APC, Yekini Nabena, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki a Abuja ranar Laraba.

Ya ce wadannan kalaman na PDP da Atiku kan tashin farashin wutan lantarki da man fetur kawai na munafunci ne.

Tashin kudin Wuta da Mai: Atiku munafikin mutum ne - Jam'iyyar APC
Tashin kudin Wuta da Mai: Atiku munafikin mutum ne - Jam'iyyar APC
Asali: UGC

KU DUBA WANNAN: Tun kan zabe, Shugaban Alkalai zai nada Alkalan kotun zaben Edo da Ondo 85

Wani sashen jawabin yace: "Masu son kasa na gaske, kungiyoyi daban-daban na tofa albarkacin bakinsu kan tashin farashin wutan lantarki da man fetur, amma mun samu jawabin jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP), da Alhaji Atiku Abubakar, suna sukan shawarar da gwamnatin Buhari ya yanke."

"Jawabin da PDP da Atiku sukayi kololuwar munafunci ne kan cigaban Najeriya."

"Babban abin takaici shine babatun dan takaran shugaban kasan PDP a zaben 2019, idan da gaske Atiku Abubakar, ya yi wadannan kalaman kamar yadda kafafen yada labarai suka wallafa."

"A lokacin yakin neman zaben 2019, babban abinda Atiku ke yakin neman zaben da shi shine idan ya hau mulki zai yi garambawul a sashen man fetur da wutan lantarki."

"Atiku ya yi jawabai a 2018 da 2019 cewa sai ya sayar da NNPC idan ya hau mulki."

"A jawabin da yayi kan sayar da NNPC, Atiku ya ce sayar da NNPC amfani zai kawo garemu. Ba zamuyi asarar komai ba, sai dai mu amfana,"

APC ta kara da cewa a watan Yuni, Atiku ya yabawa shirin shugaba Buhari na cire tallafin man fetur inda yace "daina biyan kudin tallafi ne abin da ya dace."

KARANTA: Jama'a sun suburbudi jami'in FRSC da ya ja hadari yayin kokarin kama mai laifi (Bidiyo)

Amma yanzu ya fara maganan cewa kamata yayi farashin kudin mai ya sauko, cewar APC.

APC ta ce Atiku da PDP ba su da hakkin sukan abinda shugaba Buhari ke yi saboda su suka haddasa halin da Najeriya ke ciki a yanzu sakamakon mulkin cin harawar zomo da suka yiwa kasar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel