Ba da mugun nufi na yi zanen barkwancin auren Hanan ba - Bulama

Ba da mugun nufi na yi zanen barkwancin auren Hanan ba - Bulama

- Fitaccen mai zanen barkwanci Mustapha Bulama ya yi martani a kan sukar zanen barkwancin sa da fadar shugaban kasa ta yi

- Bulama wanda ke yi wa jaridar Daily Trust aiki ya ce ba da mugun nufi ya yi zanen barkwancin ba kawai ya nuna halin ya ƴan Najeriya ke ciki ne a yanzu

- Bulama ya ƙara da cewa ya yi mamakin yadda zanen ya ɗauki hankulan mutane ya kuma yi kira ga shugabanni su rika sauƙaƙa wa talakawa rayuwa

Mustapha Bulama, mai zanen barkwanci da ke aiki tare da jaridar Daily Trust ya yi tsokaci kan sukar zanensa kan auren Hanan da fadar shugaban ƙasa ta yi.

Mai zanen barkwancin ya wallafa zanen da ya yi da ke nuna A'isha Buhari tana nuna wa ƴan Najeriya hotunan ɗaurin auren Hanan yayin da suke daf da nutsewa cikin ruwa mai dauɗa.

Ba da mugun nufi na yi zanen barkwancin auren Hanan ba - Bulama
Ba da mugun nufi na yi zanen barkwancin auren Hanan ba - Bulama
Source: Depositphotos

Zanen kuma na ɗauke da rubutu da ka cewa, "Ko ba komai za ku kalli hotuna ku ji daɗi."

KU KARANTA: Bidiyo: Amarya ta fasa auren mijinta a lokacin da aka tafi wurin daurin aure

Da ya ke tsokaci a kan zanen barkwancin, Kakakin A'isha Buhari, Aliyu Abdullahi ya ce "ba a yi musu adalci don ba wani babban shagali aka yi ba a bikin."

A bangarensa Mustapha Bulama ya ce ba da mugun nufi ya yi zanen barkwancin auren Hanan ba.

A hirar da ya yi da BBC, Bulama ya ce, "ba da mugun nufi ya yi zanen ba."

Ya ce ya yi mamakin yadda zanen barkwancin ya ɗauki hankulan mutane ya kuma yi kira ga masu rike da madafin iko su taimakawa talakawa.

Ya ce;

"Ba na da wani mugun nufi game da auren Hanan Buhari. Aiki na kawai na ke yi. Ina ƙoƙarin nuna halin ya ƴan Najeriya ke ciki ne a halin yanzu a zanen barkwancin.

"Wannan shine lokaci na farko da mutane da ke rike da manyan muƙamai a kasar suka yi magana a kan aiki na. Hakan ne nuna wadanda ke rike da mulki suna kallon mu kuma suna sauraron mu. Ina fatar za mu cigaba da zaburar da su su sawaƙa wa talakawa rayuwa."

DUBA WANNAN: Garba Shehu: An sayar da man fetur N600 kowanne lita a mulkin PDP

A wani labarin daban, Legit.ng ta ruwaito cewa Garba Shehu, Mai magana da yawun shugaba Muhammadu Buhari ya yi martani a kan ƙarin kuɗin man fetur inda ya ce an siya man fetur fiye da farashin sa na yanzu a lokacin mulkin jam'iyyar PDP.

A rubutun da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Talata, mai magana da yawun shugaban kasar ya ce har Naira 600 an siya litar man fetur a zamanin mulkin PDP.

Gwamnatin Tarayya tayi amfani da Hukumar Tallata Albarkatun Man Fetur, PPMC, a baya bayan nan ta ƙara farashin man fetur ga masu sari daga N138.62 zuwa N151.56 duk lita.

Bayan ƙarin kuɗin man fetur ɗin, ƴan kasuwa sun yi ƙarin kuɗin litar man fetur daga Naira 148 zuwa Naira 158 zuwa Naira 162 duk lita.

Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan kamfanin rarrabar da wutan lantarki na ƙasa (DisCos) ya fara aiwatar da sabon farashin wutar lantarki inda aka yi wa wasu kwastomomi ƙari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel