Yajin aikin likitoci: FG ta sanar da mummunan matakin da za ta dauka

Yajin aikin likitoci: FG ta sanar da mummunan matakin da za ta dauka

Gwamnatin tarayya ta umarci shugabanni asibitoci na tarayya da su gaggauta fara amfani da manyan likitoci da kuma masu hidimar kasa domin maye gurbin likitocin da suka tafi yajin aiki.

Ministan lafiya, Dr Osagie Ehanire, ya bada wannan umarnin a wata takarda da ya fitar a garin Abuja a ranar Laraba, jaridar The Punch ta wallafa.

Yana yin martani ne game da yajin aikin da kungiyar likitoci masu neman kwarewa suka yi a kan rashin biyansu alawus na hatsarin Covid-19 da sauran bukatunsu.

Ya ce, "Cike da matukar damuwa nake duba yajin aikin da kungiyar likitoci masu neman kwarewa suka fada a ranar Talata, 7 ga watan Satumban 2020.

"Dole ne mu tuna cewa, babban aikin likitoci da dukkan masana kiwon lafiya shine ceton rai. Fara yajin aiki a wannan lokacin da kasar da duniya ke fuskantar annoba bai dace ba.

KARANTA: Ba zamu taba kyale mujallar da ta wallafa hoton Annabi Muhammad ba a kasar Faransa - Ayatollah Khamenei

Yajin aikin likitoci: FG ta sanar da mummunan matakin da za ta dauka
Yajin aikin likitoci: FG ta sanar da mummunan matakin da za ta dauka. Hoto daga The Punch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Dan wasan kwallon kafa a Najeriya ya fadi ya mutu a tsakiyar fili yayin da yake buga wasa

"A wannan lokacin na tsanani ne dukkan masana kiwon lafiya ya kamata su dage wurin shawo kan manyan matsalolinmu, wanda shine cutar korona mai barazana ga dan Adam.

"Gaskiya wannan yajin aikin na da matukar cin rai. Baya ga haka, bukatunsu suna da yawan da ba za mu iya cika duka ba. Da za su kara hakuri, da komai ya zo da sauki.

"Ma'aikatar lafiya ta tarayya don haka ta gane cewa ya zama dole ta samo dabarun da za su hana jama'a fuskantar kalubalen yajin aikin.

"Tana kira ga dukkan shugabannin ma'aikatun lafiya na tarayya da su cigaba da tabbatar da kiyaye dokokin dakile yaduwar cutar korona da aka aike musu.

“A gaggauta ci gaba da ganin marasa lafiya. Kwararrun likitoci da likitoci masu hidimtawa kasa su ci gaba da aiki."

Legit.ng ta ruwaito cewa, kungiyar NARD ta likitocin da ke neman kwarewa a aiki ta ce yajin da ta daka zai soma aiki ne a yau Litinin, 7 ga watan Satumba, 2020.

Likitocin asibitocin kasar za su tafi yajin aiki a sakamakon gaza zama da shugabanninsu da gwamnatin tarayya ta yi a ‘yan kwanakin bayan nan.

Bayan tafiya yajin aiki, kungiyar NARD ta yi kira ga sauran kungiyoyin ma’aikatan asibiti ta mara mata baya a wannan gwagwarmaya da ta ke yi.

Kungiyar NARD ta bukaci ungonzoma da masu bada magani da sauran likitoci su amsa wannan kira domin ganin an kara yawan alawus din da ake ba su.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel