Tun kan zabe, Shugaban Alkalai zai nada Alkalan kotun zaben Edo da Ondo 85

Tun kan zabe, Shugaban Alkalai zai nada Alkalan kotun zaben Edo da Ondo 85

- Zabukan Najeriya a kwanakin nan ba su karewa a akwati, sai an garzaya kotu

- Kusan dukkan zabukan gwamnan da aka gudanar a 2019, sai da aka garzaya kotu

- Shugaban Alkalai zai nada Alkalai har 85 don zama kan zabukan gwamnann Edo da na Ondo da za'a gudanar

Shugaban Alkalan Najeriya, Alkali Tanko Mohammed, zai rantsar da Alkalai 85 domin zama a kotun zabukan gwamnan da zasu gudana a jihar Edo da Ondo da kuma na maye gurbin yan majalisa da suka mutu a sassan Najeriya.

Jami'ar yada labaran kotun daukaka kara, Sa'adatu Kachalla, ta bayyana a jawabin da ta saki cewa za ayi bikin rantsar da su ne a dakin taron kotun koli ranar Alhamis a Abuja.

Kotun daukaka kara ce hedkwatar sauraron karan zabe kuma shugabar kotun, Alkali Monica Dongban-Mensem, ce ke da hakkin zaben Alkalan da zasu zauna kan kowani kara.

Za'a gudanar da zaben jihar Edo ranar 19 ga Satumba, 2020, yayinda za'ayi na jihar Ondo ranar 10 ga Oktoba, 2020.

Bayan zaben da sanar da wanda yayi nasara, duk dan takaran da bai amince da sakamakon ba na da kwanaki 21 domin shigar da kara kotun zabe.

Duk wanda bai shigar da kara ba har bayan kwanaki 21 da aka sanar da sakamako, ba zai samu damar shigarwa ba.

Jawabin Kachalla yace, "Shugaban Alkalai a ranar Alhamis, 10 ga Satumba, 2020 zai rantsar da Alkalai 85 domin shari'a kan kararrakin zabukan dake tafe a jihar Edo ranar 19 ga Satumba, da Ondo, 10 ga Ondo da kuma zabukan maye gurbi da INEC ta shirya."

"Lokaci: karfe 2 na rana, a dakin taron kotun koli."

"Bayan haka Shugabar kotun daukaka kara Justice Monica Dongban-Mensem, za ta shirya taron horar da Alkalan 85."

Tu kan zabe, Shugaban Alkalai zai nada Alkalan kotun zaben Edo da Ondo 85
Tu kan zabe, Shugaban Alkalai zai nada Alkalan kotun zaben Edo da Ondo 85
Source: UGC

DUBA NAN: Jama'a sun suburbudi jami'in FRSC da ya ja hadari yayin kokarin kama mai laifi (Bidiyo)

A bangare guda, Gwamna Godwin Obaseki ya bayyana cewa zai dauki kaddara idan har ya sha kaye a zabe na gaskiya da adalci.

Obaseki ya bayyana hakan ne a yayinda ya zanta da manema labarai bayan ya ziyarci sufeto janar na yan sanda, Mohammed Adamu a hedkwatar rundunar da ke Abuja.

Ya ce a matsayinsa na dan damokradiyya, zai karbi sakamakon zabe na gaskiya, inda ya kara da cewa: “amma daga dukkanin alamu a yau, ina da tabbacin yin nasara.”

Sai dai kuma ya nuna damuwa game da tsaron masu zabe a jihar Edo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel