Dan Najeriya da ya ki karbar cin hancin $6m ya samu lambar yabo

Dan Najeriya da ya ki karbar cin hancin $6m ya samu lambar yabo

Gidauniyar Akinde Adeosun (AAF), ta bada lambar yabo da jinjina ta shugabancinta na 2020 ga manajan daraktan farko na kamfanin hakar man fetur na Shell da ke Najeriya, Dr Olufemi Lalude.

Wannan yana zuwa bayan da Lalude, wanda injiniya ne ya yi fatali da cin hancin dala miliyan shida wacce aka yi masa tayi, gidauniyar ta sanar da hakan a ranar Laraba a Legas.

Lambar yabon wacce suka saka wa suna, "Nagarta a shugabanci" an mika ta ga Lalude wanda yanzu yake da shekaru 81 a taron kungiyar na wannan shekarar.

A yayin jawabi a taron wanda aka yi ta yanar gizo, Akinjide Adeosun, shugaban AAF, ya ce sun yaba wa Lalude saboda nagarta ce tushen gidauniyarsu, Daily Nigerian ta wallafa.

Gidauniyar ta yadda da cewa, rayuwa za ta saukaka ga kowa matukar kasar nan ta ci gaba da samun nagartattun shugabanni a kowanne fanni.

"Nagarta babban jigo ce wacce kowacce al'umma za ta iya ginuwa a kai kuma ta tsaya. Gaskiya, rikon amana, mutunta jama'a, aiki tukuru duk suna daga cikin nau'in nagarta.

KU KARANTA: Kashe-kashe: CAN da shugabannin kudancin Kaduna sun ki halartar taron sasanci

Dan Najeriya da ya ki karbar cin hancin $6m ya samu lambar yabo
Dan Najeriya da ya ki karbar cin hancin $6m ya samu lambar yabo. Hoto daga Daily Nigerian
Source: Facebook

KU KARANTA: Ba zamu taba kyale mujallar da ta wallafa hoton Annabi Muhammad ba a kasar Faransa - Ayatollah Khamenei

"A shekaru masu yawa da suka gabata, gwarzonmu kuma dattijon arziki, Olufemi Lalude, an bashi tayin cin hancin dala miliyan shida.

"Kungiyar da ta bashi wannan cin hancin ta yi kokarin yi masa barazana amma haka ya tsaya tsayin daka.

"An maka shi a kotu tare da wanda yake wa aiki amma yayi nasara. Lalude mutum ne mai nagarta kuma irinsu kadan ne da ke disashe rashawa.

"A yau yana cika shekaru 81 cike da natsuwa, jin dadi da kuma rayuwa mai cike da wadatar zuci," Yace.

Ya kara da cewa, "Muna taya shi murna a yau. Ya fara aikinsa da nagarta a cikin zuciyarsa.

"Muna da jama'a nagari a Najeriya. Dole ne mu taya murna ga wanda ya yi kokarin ganin karshen rashin gaskiya."

A wani labari na daban, wani faifan bidiyo da ke yawo a dandalin sada zumunta na intanet ya nuna wasu jami'an 'yan sanda suna kama abokan aikinsu saboda laifin karbar cin hanci.

Jami'an 'yan sandan Najeriya ta runduna ta musamman na 'Operation Puff Adder' ne suka isa wurin da abin ke faruwa a cikin motarsu ta sintiri kuma suka kama 'yan sandan da ke karbar rashawar a unguwar Ijesha da ke Legas.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel