Fittacen fasto na ƙasar Ghana ya bindige matarsa har lahira a Amurka

Fittacen fasto na ƙasar Ghana ya bindige matarsa har lahira a Amurka

An kama wani fitaccen fasto ɗan asalin ƙasar Ghana mazaunin Amurka Sylvester Ofori bayan ya bindige matarsa, Barbara Tommey har lahira.

Lamarin ya faru ne a harabar wurin da matar ke aiki a Navy Federal Credit Union kusa da Kanti a Millenia Orlando a ranar Talata 8 ga watan Satumban 2020.

Kakakin ƴan sandan Orlando ya ce Sylvester ya harbi Barbara ne a kusa da Gardens Park kafin ƙarfe 9 na safe.

Fittacen fasto na ƙasar Ghana ya bindige matarsa har lahira a Amurka
Fittacen fasto na ƙasar Ghana ya bindige matarsa har lahira a Amurka. Hoto daga LIB
Asali: Twitter

An tabbatar da mutuwar Barbara a wani asibiti da ke Orlando jim kaɗan bayan an garzaya da ita asibitin.

An kama mijin ta, Ofori, mai shekaru 35 a yammacin ranar Talata a cewar Kakakin ƴan sandan.

DUBA WANNAN: Mutum biyu sun riga mu gidan gaskiya sakamakon harin da ƴan IPOB suka kai wa hausawa a Rivers

Yana tsare a gidan yari na Orange County inda ake tuhumarsa da laifin kisar gilla da bindiga.

Yayin jawabin manema labarai da ya yi a safiyar Talata, shugaba yan sandan Orlando, Rolon ya ce na'urar daukan bidiyon ta CCTV ta naɗa harbin.

Fittacen fasto na ƙasar Ghana ya bindige matarsa har lahira a Amurka
Fittacen fasto na ƙasar Ghana ya bindige matarsa har lahira a Amurka. Hoto daga LIB
Asali: Twitter

"Kana iya ganin ta yi mamakin abinda ke faruwa," in ji shi.

Navy Credit Union ta fitar da jawabi game da harbin inda ta yi wa iyalan mamaciyar jaje ta kuma ce za ta cigaba da ɗaukan matakan kare ma'aikatan ta.

Rahotanni sun ce Fasto Sylvester ya daɗe yana cin zarafin matarsa. Hakan yasa iyalan ta suka bata shawarar ta rabu da shi.

Amma Sylvester ya bi ta har wurin da ta ke aiki ya harbe ta da bindiga sau bakwai kamar yadda LIB ta ruwaito.

Fittacen fasto na ƙasar Ghana ya bindige matarsa har lahira a Amurka
Fittacen fasto na ƙasar Ghana ya bindige matarsa har lahira a Amurka. Hoto daga LIB
Asali: Twitter

KU KARANTA: Faɗa a gidan yari: Fursuna ya datse yatsun gandireba ya haɗiye a Italy

Wata mata mai suna Lisa da abin ya faru a idon ta ta ce, "Har yanzu ban dawo cikin hayyaci na ba, har yanzu ban watsake ba."

Ta ce ta ga lokacin da Barbara ta fito waje za ta shiga motar ta kafin a harbe ta.

"Kawai sai na ga ya daga hannunsa riƙe da bindiga ya harbe ta," in ji ta.

"A baya-baya ya riƙa bin ta. Ban san ko ta san yana bayan ta ba. Na fara gudu, ina cikin gudun na sake jin ƙarar harbi sau uku zuwa huɗu."

Lisa ta ce marigayiyar mutumiyar kirki ce.

Ta ce, "Tana tarba ta da kyau duk lokacin da na zo bankin. Tana da kirki sosai."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel