NLC ga Lai Mohammed: Ba kudin man fetur muke korafi ba, karancin albashi ne matsalarmu

NLC ga Lai Mohammed: Ba kudin man fetur muke korafi ba, karancin albashi ne matsalarmu

Ayuba Wabba, shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC), ya ce gwamnatin tarayya ba ta fahimcesu ba a kan korafin da suka yi na tashin gwauron zabin da farashin man fetur yayi a Najeriya.

A ranar Litinin da ta gabata, ministan yada labarai ya ce duk da karin farashin litar man fetur da gwamnati tayi, har yanzu farashin shine mafi karanci a fadin nahiyar Afrika.

A yayin zantawa da jaridar The Punch, Wabba yace gwamnatin kafin ta fara komai kamata yayi ta duba yadda darajar naira ke kara lalacewa, sannan ta duba nawa take biyan ma'aikatanta a matsayin mafi karancin albashi a Najeriya.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe dan sanda 1, sun raunata wasu hudu

NLC ga Lai Mohammed: Ba kudin man fetur muke korafi ba, karancin albashi ne matsalarmu
NLC ga Lai Mohammed: Ba kudin man fetur muke korafi ba, karancin albashi ne matsalarmu. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

Wabba yace kwata-kwata ba a duba wannan ba kuma idan aka duba karin farashin wutar lantarki da kayan abinci, abun takaici ne duka.

"Wannan kamanceceniyar ba za ta yuwu ba saboda faduwar darajar kudin kasar nan. Gashi a kowacce rana sake lalacewa take.

"Idan sauran kasashen suna da kudi mai daraja, babu shakka ko nawa ne karancin albashinsu karin farashin kayayyaki ba zai damesu ba," Wabba yace.

"Ba kayayyakin man fetur kadai suka tashi ba, hatta kayan abinci sun yi tsada a Najeriya saboda faduwar darajar Naira.

"Ko za su iya kamanta darajar Naira da sauran kudaden nahiyar Afrika a cikin shekarun nan da kuma rashin daidaituwarta a shekaru biyar da suka gabata? Za ku iya amsawa?" Wabba ya tambaya.

Ya ce, gwamnatin bata nuna tausayinta ba ta yadda ta kara kudin litar man fetur tare da na wutar lantarki a lokaci daya. Ya ce an kai 'yan Najeriya bango.

KU KARANTA: Yadda jami'ai suka yi wa matashiya fyade a motar kaita asbiti bayan kamuwa da korona

Idan za mu tuna, a ranar 1 ga watan Satumban 2020, gwamnatin tarayya ta kara farashin man fetur zuwa N162 a duk lita daya.

Ministan ya bayyana hakan a yayin jawabi ga manema labarai na hadin guiwa wanda ministan wutar lantarki, Saleh Mamman da karamin ministan man fetur, Timipre Sylva suka hada.

Mohammed ya ce , duk da halin da tattalin arzikin kasar nan ke ciki, gwamnati ta ci gaba da aiwatar da manyan ayyukanta ballantana biyan albashi. Amma kuma dole ne ta cire wa kanta al'adun da za su durkusar mata da tattalin arzikinta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel