Bayan shekaru 5: Gwamnatin Kogi ta shirya gudanar da zaben kananan hukumomi

Bayan shekaru 5: Gwamnatin Kogi ta shirya gudanar da zaben kananan hukumomi

- Gwamnatin jihar Kogi za ta gudanar da zaben kananan hukumomin jihar a cikin watan Disamba, karon farko bayan shekaru biyar

- Tun a zangon farko na gwamnatin Yahaya Bello, kungiyoyi da jam'iyyun adawa ke matsawa gwamnatin lamba na gudanar da zaben

- Hukumar gudanar da zaben jihar (KSIEC) ta sanar da cewa za su fara karbar takardun tsayawa takara daga ranar 24 ga watan Satumba zuwa ranar 2 ga watan Oktoba

Ma damar ba a samu wani canji ba, to gwamnatin jihar Kogi za ta gudanar da zaben kananan hukumomin jihar a cikin watan Disamba, karon farko bayan shekaru biyar.

Shugaban hukumar gudanar zabe na jihar (KSIEC), Mamman Nd Eri, ya sanar da ranar 12 ga watan Disamba, 2020 a matsayin ranar gudanar da zaben kananan hukumomin.

A taron masu ruwa da tsaki a garin Lokoja, babban birnjin jihar, Mamman Eri ya tabbatar da cewa an dauki matakai na ganin cewa an samu nasarar yin zaben.

Ya jaddada cewa jam'iyyu za su fara karbar takardun tsayawa takara daga ranar 24 ga watan Satumba zuwa ranar 2 ga watan Oktoba.

KARANTA WANNAN: Zaben Edo: APC ta zargi Obaseki da cin mutuncin Sarkin Benin

Bayan shekaru 5: Gwamnatin Kogi ta shirya gudanar da zaben kananan hukumomi
Bayan shekaru 5: Gwamnatin Kogi ta shirya gudanar da zaben kananan hukumomi
Source: Twitter

Sannan za a gudanar da zaben fitar da gwani na jam'iyyun, da kuma warware rikice rikice da ka iya tasowa bayan zaben fitar da gwanin a ranar 6 ga watan Oktoba.

Shugaban hukumar zaben ya kuma ce jam'iyyun za su mika takardun yan takararsu a shelkwatar hukumar a ranar 19 ga watan Oktoba.

Ya ce za a tantance takardun 'yan takarar , a ranar 27 ga watan Oktoba da kuma 3 ga watan Nuwamba, 2020.

Gwamnatin Yahaya Bello a jihar, wacce ta ke cikin shekarar farko a mulkinta karo na biyu, ta gaza gudanar da zaben kananan hukumomin duk da zanga zangar kungiyoyi da mutane.

KARANTA WANNAN: Yadda muka kashe gagararren dan ta'adda, Terwase Gana - Rundunar soji

Haka zalika, jam'iyyun adawa da masu ruwa da tsaki a jihar sun sha matsawa gwamnatin lamba akan ta gudanar da zaben kananan hukumomin.

Sai dai, gwamnatin ta kasance tana dora shuwagabannin rikon kwarya, domin jan ragamar ayyukan kananan hukumomin jihar, tsawon shekaru biyar din nan.

Mafi akasari, masu tallafawa gwamnan na musamman (SSA) ne ke shugabantar kananan hukumomi 21 na jihar.

A yayin taron hukumar zaben, kwamishinan 'yan sanda na jihar, CP Ayuba Ede ya ba da tabbacin samar da tsaro a jihar, a yayin gudanar da zaben da kuma bayan zaben.

Ya jaddada cewa rundunar 'yan sandan za ta yi duk mai yiyuwa don ganin cewa an gudanar da zaben cikin lumana ba tare da tashin hankula ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel