Zaben Edo: APC ta zargi Obaseki da cin mutuncin Sarkin Benin

Zaben Edo: APC ta zargi Obaseki da cin mutuncin Sarkin Benin

- Jam'iyyar APC ta yi zargin cewa akwai alakar Gwamna Obaseki da wani rubutu na cin mutunci da zagin Sarkin Benin

- Jam'iyyar ta yi ikirarin cewa cin mutuncin Basaraken ya fara ne daga ranar 2 ga watan Satumba a taron sasanci da aka yi a jihar

- Sai dai mai magana da yawun Obaseki ya nisanta gwamnan daga wannan rubutu da APC ta ke kafa hujja da shi

Jam'iyyar APC ta zargi gwamnan jihar Edo mai ci a yanzu, Godwin Obaseki da cin mutuncin Sarkin Benin, Ewuare II, da kuma yi masa zagin wulakanci.

Jam'iyyar APC reshen jihar Edo a cikin wata sanarwa ta zargi gwamnan da daukar nauyin yin batanci da kalaman cin mutunci ga Sarkin Benin a kafofin sada zumunta.

Prince John Mayak, shugaban yakin zaben APC a yanar gizo na jihar Edo ya yi ikirarin cewa an fara batanci ga Sarkin Benin a kafofin sada zumunta tun daga ranar 2 ga watan Satumba, 2020.

A ranar ne Sarkin ya kira gaba daya 'yan takarar gwamna daga jam'iyyu daban daban na jihar, inda aka yi zaman sulhu don wanzar da zaman lafiya a lokacin zaben.

KARANTA WANNAN: Yadda muka kashe gagararren dan ta'adda, Terwase Gana - Rundunar soji

Zaben Edo: APC ta zargi Obaseki da cin mutuncin Sarkin Benin
Zaben Edo: APC ta zargi Obaseki da cin mutuncin Sarkin Benin
Source: Depositphotos

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa jam'iyyar ta ce al'ummar jihar Edo za su ladabtar da Obaseki akan cin mutuncin Sarkinsu, ta hanyar korarshi daga kujerar a zaben jihar da za ayi ranar 19 ga watan Satumba.

Sai dai mai magana da yawun Obaseki ya nisanta gwamnan da wannan rahoto da jam'iyyar APC ke yadawa na cewar ya dauki nauyin cin mutuncin Sarkin Benin.

Hadimin gwamnan ta fuskar watsa labarai, Crusoe Osagie ya jaddada cewa babu alakar gwamnan da duk wasu kalaman batancin da aka yi a kafofin sada zumunta.

Ya ce gwamnan jihar Edo na nuna tsantsar girmamawarsa da mutunta Basaraken kuma bai taba nuna alamar wulakanta Sarkin na Benin ba.

Osagie ya ce wasu masu son zuciya ne kawai ke son alakanta gwamna jihar Edon da rubuce rubucen batancin da ake yi saboda wata bukatarsu ta siyasa.

KARANTA WANNAN: Zuwan COVID-19 wa'azine a garemu, ya kamata mu koma ga Allah - Gwamna Sanwo-Olu

A wani labarin, wani masoyin Gwamna Godwin Obaseki kuma marubuci, Lukman Akemokue, ya ce dan takarar APC, Osagie Ize-Iyamu, da Adams Oshiomhole za su sha kayi a hannun PDP.

A cewar Akemolue, dukkan alamomi sun bayyana, da ke nuni da cewa Gwamna Obaseki ne zai samu nasara a zaben gwamnan jihar da za ayi a ranar 19 ga watan Satumba.

Akemokue wanda ya zanta da manema labarai a Benin City, babban birnin jihar, ya ce Gwamna Obaseki ba wai yana takara da Osagie Ize-Iyamu ba ne, yana takara da Oshiomhole ne.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel