Jaruman matasa 3 da suka ƙwaci kansu daga hannun masu garkuwa a Katsina sun samu kyauta daga gwamnati

Jaruman matasa 3 da suka ƙwaci kansu daga hannun masu garkuwa a Katsina sun samu kyauta daga gwamnati

Gwamnatin jihar Katsina da rundunar ƴan sanda sun karrama wasu matasa saboda jarumtar da suka nuna na ƙwatar kansu daga hannun yan bindiga har ma sun kashe ɗaya.

An kuma bawa matasan; maza biyu da mace ɗaya kyauta saboda mayarwa yan sanda bindiga da adda da suka ƙwato daga hannun ƴan bindigan.

Kwamishinan ƴan sanda na jihar Katsina, Sanusi Buba ya bawa matasan kyautan kuɗi a madadin gwamantin jihar da rundunar.

Jaruman matasa 3 da suka ƙwaci kansu daga hannun masu garkuwa a Katsina sun samu kyauta daga gwamnati
Jaruman matasa 3 da suka ƙwaci kansu daga hannun masu garkuwa a Katsina sun samu kyauta daga gwamnati. Hoto daga The Punch
Asali: Twitter

An bawa matasan kyautan kudaden ne a ranar Talata a ofishin kwamishinan ƴan sandan saboda kada a jefa su cikin hastari.

KU KARANTA: Faɗa a gidan yari: Fursuna ya datse yatsun gandireba ya haɗiye a Italy

Kwamishinan ƴan sandan kuma bai bayyana sunayen matasan ba da garuruwan su amma wadanda suka hallarci taron sun ga matasan.

Kwamishinan ƴan sandan ya kuma gabatarwa mutane bindigar ƙirar Ak-47 da addar da matasan suka kwato daga hannun ƴan bindigan.

A cewar kwamishinan, matasan sun yi jarumta sun fi ƙarfin yan bindigan da suka sace su daga gonakin su.

Babba daga cikin matasan ya bayar da labarin arrangamarsu da ƴan bindigan a wurin taron.

DUBA WANNAN: Boko Haram ta kashe mutum huɗu yayin da suke barci, ta ƙona wasu uku da ransu a Borno

Ya ce, "Ƴan bindigan da farko sun yi garkuwa da matasan biyu da mace ɗaya a gonarsu. Matasan daga bisani suka yi jarumta suka kwaci kansu. Ɗaya ya tinkari mai bindigan yayin da ɗayan ya tinkari mai addar.

"Wanda ya tinkari mai addar ya ci galaba a kansa ya koma ya taimaka wa wanda ke kokowa da mai rike da bindigan shima suka yi galaba a kansa.

"Ɗaya daga cikin matasan ya samu rauni a kai duk da cewa ɗaya daga cikin ƴan bindigan ya mutu yayin da ɗayan ya tsere.

"Matasan uku sun nuna kishin kasa suka mika makaman wato Ak-47 da adda ga yan sanda bayan afkuwar lamarin.

"Saboda jarumtarsu da kishin ƙasa ne yasa gwamantin jiha da rundunar ƴan sanda suka basu tukwuici."

A wani rahoton daban kunji hausawa biyu mazauna Oyigbo a ƙaramar hukumar Oyigbo ta jihar Rivers ne suka rasu sakamakon harin da wasu da ake zargin ƴan kungiyar masu fafutikan kafa ƙasar Biafra, IPOB, suka kai musu a Oyigbo.

Wani ganau ya bayyana cewa fusatattun mambobin na ƙungiyar IPOB sun kai wa Hausawa mazauna Oyigbo hari a ranakun Asabar da Lahadi.

Ganau ɗin ya ce an kashe aƙalla mutane biyu yayin da wasu da dama sun samu munannan raunuka kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel