Garkuwa: An yanke wa wasu mutum 5 hukuncin kisa ta hanyar rataya a Rivers

Garkuwa: An yanke wa wasu mutum 5 hukuncin kisa ta hanyar rataya a Rivers

Babban kotun da ke zaman ta a Fatakwal a jihar Rivers ta yanke wa mutum biyar hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda garkuwa da kashe wani Mista Anthony Okoro.

An samu mutum biyar cikin bakwai da aka gurfanar a kotu da laifuka 10 da suka hada da hadin baki, sata, fashi da makami, garkuwa da kisa.

Sufeta Janar na ƴan sandan Najeriya ne ya shigar da ƙarar a kotu cikin takarda mai lamba PHC/324/2017. Wadanda aka yanke wa hukuncin sun hada da Ouchi Charles, Miracle Anumuna, Ifeanyi Simon Koko Basset da Uchenna Stanley Amaechi.

Garkuwa: An yanke wa wasu mutum 5 hukuncin kisa ta hanyar rataya a Rivers
Garkuwa: An yanke wa wasu mutum 5 hukuncin kisa ta hanyar rataya a Rivers. Hoto daga LIB
Source: Twitter

Kotun ta wanke sauran mutane biyun da aka ambata a karar; Chukwudi Etete da Anthony Ugwu an kuma sake su.

KU KARANTA: Boko Haram ta kashe mutum huɗu yayin da suke barci, ta ƙona wasu uku da ransu a Borno

Wadanda aka samu da laifin, a ranar 26 ga watan Mayun 2016 sun kai wa Anthony Okoro hari a gidansa da ke Woji a Fatakwal suka harbe shi suka tafi da gawarsa.

An kuma ce sun sace motarsa Range Rover Jeep, Kia Optima, Talabijin, wayar salula ƙirar infinix da sauran abubuwa masu muhimmanci mallakar Okoro.

Da ya ke zartar da hukunci, Mai Shari'a George Omeraji ya ce wanda suka shigar da ƙarar sun gamsar da kotu cewa wadanda ake zargin sun aikata laifin.

DUBA WANNAN: Mutum biyu sun riga mu gidan gaskiya sakamakon harin da ƴan IPOB suka kai wa hausawa a Rivers

Alƙalin ya saki Etete da Ugwu inda ya ce masu shigar da ƙarar ba su iya gamsar da kotu cewa suna da masaniya a kan laifin ba sai dai cikin kuskure sun siya wayoyin mamacin.

Ya ce masu shigar da ƙarar sun gabatar da hujjoji da ke nuna wanda ake yanke wa hukuncin sun hadu a Unguwar Genesis sun tsara yadda za su sace Okoro su kashe shi.

Ya kara da cewa wanda suka shigar da ƙarar sun gamsar da kotu cewa wadanda aka yanke wa hukuncin ne suka yi sanadin kisar Okoro

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, kwamishinan ƴan sanda na jihar Gombe, Shehu Maikudi a ranar Litinin ya gabatar wa manema labarai wasu masu safarar mutane huɗu da ƙananan yara 12.

Maikudi ya ce yan sanda sunyi nasarar kama yan kungiyar ne tare da hadin kai da taimakon iyayen yaran kamar yadda The Punch ta ruwaito.

A cewar Maikudi, wasu daga cikin iyayen sun shigar da rahoto cewa an sace yaransu. An kama daya daga cikin wadanda ake zargin a makon da ta gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel