Abinda muke bukata domin magance ta'addanci da 'yan bindiga - CAS

Abinda muke bukata domin magance ta'addanci da 'yan bindiga - CAS

Shugaban dakarun sojin saman Najeriya, Air Marshal Sadique Abubakar, ya ce bayanan sirri sune abinda ake bukata matukar ana bukatar nasara a yaki da ta'addanci da 'yan bindiga a fadin kasar nan.

Ya sanar da hakan a ranar Talata, yayin bikin yaye hafsin sojin da aka horar wurin samo bayanan sirri a kwalejin tsaro da ke Karu, Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Kamar yadda yace, bayanan sirri masu kyau sune jigo kuma nasarar kowanne aiki, ballantana a samamen da ake kaiwa ta jiragen yaki, "wanda illar rashinsa ko kuskure yana iya zama babbar matsala".

Ya jaddada cewa, ta hanya daya kadai ake samun wadannan bayanan masu ingaci shine ta gogaggun ma'aikata masu horo mai inganci.

KU KARANTA: Yadda jami'ai suka yi wa matashiya fyade a motar kaita asbiti bayan kamuwa da korona

Ya ce an yi matukar kokari wurin horar da matasan hafsin sojan, kuma an koyar da su dukkan dabaru da ilimin da suke bukata wurin shawo kan matsalar tsaron cikin gida.

"Dalilin da yasa aka zabi wadannan sojojin aka koyar da su samo bayanai shine, tunanin yadda za a samu jami'ai wadanda za su iya taimakawa rundunar sojin saman Najeriya wurin sauke nauyin da ke kanta," yace.

Abubakar ya yi kira ga sojin da ake yayewa da su yi amfani da dukkan dabarun da suka koya wurin amfanin kasa baki daya.

Ya ce su kasance wadanda kishin kasa suka saka a gaba tare da da'a domin gujewa abinda zai bata sunansu da na aikinsu.

Abinda muke bukata domin magance ta'addanci da 'yan bindiga - CAS
Abinda muke bukata domin magance ta'addanci da 'yan bindiga - CAS. Hoto daga Daily Trust
Source: Twitter

KU KARANTA: Hotuna: Ma'aikatan da suka yi murabus sun hana shiga da fita a gidan gwamnatin Delta

A wani labari na daban, A ranar Talata, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana martanin da yayi wa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, a kan zarginsa da yayi da kashe Kiristoci.

A ranar 30 ga watan Afirilun 2018, Buhari ya gana da Trump a birnin Washington domin tattaunawa a kan ta'addancin Boko Haram, tattalin arziki da sauransu.

A jawabinsa na taron da yayi da ministoci a fadarsa da ke Abuja a yau Talata, Buhari ya ce ya sanar da takwaransa na kasar Amurka cewa rikicin makiyaya da manoma ba na addini bane.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel