Garba Shehu: An sayar da man fetur N600 kowanne lita a mulkin PDP

Garba Shehu: An sayar da man fetur N600 kowanne lita a mulkin PDP

Garba Shehu, Mai magana da yawun shugaba Muhammadu Buhari ya yi martani a kan ƙarin kuɗin man fetur inda ya ce an siya man fetur fiye da farashin sa na yanzu a lokacin mulkin jam'iyyar PDP.

A rubutun da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Talata, mai magana da yawun shugaban kasar ya ce har Naira 600 an siya litar man fetur a zamanin mulkin PDP.

Gwamnatin Tarayya tayi amfani da Hukumar Tallata Albarkatun Man Fetur, PPMC, a baya bayan nan ta ƙara farashin man fetur ga masu sari daga N138.62 zuwa N151.56 duk lita.

Garba Shehu: An sayar da man fetur N600 kowanne lita a mulkin PDP
Garba Shehu: An sayar da man fetur N600 kowanne lita a mulkin PDP. Hoto daga The Cable
Source: UGC

DUBA WANNAN: Bidiyo: Amarya ta fasa auren mijinta a lokacin da aka tafi wurin daurin aure

Bayan ƙarin kuɗin man fetur ɗin, ƴan kasuwa sun yi ƙarin kuɗin litar man fetur daga Naira 148 zuwa Naira 158 zuwa Naira 162 duk lita.

Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan kamfanin rarrabar da wutan lantarki na ƙasa (DisCos) ya fara aiwatar da sabon farashin wutar lantarki inda aka yi wa wasu kwastomomi ƙari.

Yan Najeriya da kungiyoyi da dama sun yi tir da ƙarin. Cibiyar demokradiyya da cigaba (CDD) ta ce gwamnati ba ta yi komai ba domin taimakawa mutane su huce raɗaɗin annobar korona.

Jam'iyyar adawa ta PDP ta ce ƙarin kudaden 'zalunci ne da hora' ƴan Najeriya ta kuma bukaci a janye ƙarin kuɗaɗen.

Amma Shehu ya ce jam'iyyar hamayyar tana ruɗar mutane ne kawai.

KU KARANTA: Mun gaji da jan kafa da ka ke yi, ka canja shugabannin tsaro: Hadakar kungiyoyin arewa ga Buhari

"Kada ku bari PDP ta ruɗe ku. A lokacin da ake wuyan man fetur, sun siyar da litar man fetur a kan N600 a ranar bikin Easter a shekarar 2013 (Ku duba jaridar Punch da aka wallafa a ranar)," ya kuma saka hoton jaridar da aka wallafa a ranar.

Sai dai ma'abota amfani da shafukan sada zumunta na Twitter sun bayyana ra'ayoyin su mabanbanta a kan abinda Shehu ya ce.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa kun ji shima tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya soki karin kudaden man fetur da lantarki da aka yi a kasar.

Ya bayyana karin a matsayin matakan da aka dauka ba tare da yin shawara ba duba da halin rashin kudi da galabaita da yan kasar ke ciki sakamakon annobar korona.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel