Yanzu-yanzu: Bayan amsan kudin fansa, yan bindiga sun kashe jami'in tsaro da dalibar makaranta a Kaduna

Yanzu-yanzu: Bayan amsan kudin fansa, yan bindiga sun kashe jami'in tsaro da dalibar makaranta a Kaduna

Jami'in hukumar sibil defens NSCDC, Bulus Sanda, da masu garkuwa da mutane suka sace tare da wasu dalibai kwanaki goma da suka gabata sun rigamu gidan gaskiya.

An sace Bulus Sanda tare da wasu mutane uku, lokacin da yan bindiga suka kai hari gidajensu dake Mararaban Rido a jihar Kaduna ranar 28 ga Agusta, 2020.

Majiya daga iyalansa ta bayyana cewa an kasheshi ne ranar Talata bayan amsan makudan kudi na fansa.

"Mun biya kudin fansa kuma muna jiran a sake shi. Amma bayan wani dan lokaci, sai suka kiramu cewa sun kashehi saboda sun samu labarin cewa jami'in tsaro ne," majiyar ta bayyana.

"Sun fada mana inda suka jefar da gawarsa. Wannan abin takaici ne, lamarin tsaro yanzu ya zama abin tsoro kuma babu abinda gwamnati keyi don magance hakan."

Kwamandan hukumar NSCDC na jihar Kaduna, Babangida Dutsinma, wanda ya tabbatar da labarin kisan ya ce ba'a dade da tura marigayin jihar Kaduna ba.

Ya ce Bulus Sanda ya shiga aikin a shekarar 2010.

Ya aika sakon ta'azziya zuwa ga iyalan marigayin kuma yayi addu'an Allah ya kara musu hakuri.

DUBA NAN: Kashe-kashe: CAN da shugabannin kudancin Kaduna sun ki halartar taron sasanci

Yanzu-yanzu: Bayan amsan kudin fansa, yan bindiga sun kashe jammi'in tsaro da dalibar makaranta a Kaduna
yan bindiga sun kashe jammi'in tsaro da dalibar makaranta a Kaduna
Source: UGC

KU KARANTAN WANNAN: Mun shirya yin sulhu yanzu a jihar Zamfara amma akwai matsala guda - AbdulAziz Yari

Mun kawo muku rahoton cewa a ranar Juma'a wasu 'yan bindiga suka afkawa garuruwan Mararraban Rido da Juji da ke a karamar hukumar Chikun, jihar Kaduna, inda suka kashe mutane biyu.

Yan bindigar sun kashe mutane biyu a Juji, ya yin da suka afkawa garin Maraban Rido, inda suka yi awon gaba da mutane hudu ciki har da dan sanda, maras lafiya.

An shaidawa manema labarai cewa daga cikin wadanda aka sace a harin da suka kai, har da yarinya mai shekaru 14, jami'in NSCDC da kuma mai gadi.

Wata majiya ta shaida cewa 'yan bindigar sun fara kai harin ne a gidan shugaban kungiyar CAN reshen karamar hukumar Kaduna ta Arewa, Rev. Elisha Abu kafin shiga wasu gidajen.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel