Kashe-kashe: CAN da shugabannin kudancin Kaduna sun ki halartar taron sasanci

Kashe-kashe: CAN da shugabannin kudancin Kaduna sun ki halartar taron sasanci

Kungiyar Kiristoci ta kasa reshen jihar Kaduna (CAN) tare da shugabannin kungiyoyin Kiristoci na kudancin Kaduna, a ranar Talata sun ki halartar taron sasanci da aka yi a Kafanchan, karamar hukumar Jema'a ta jihar Kaduna.

Taron da aka yi a yau Talata, yana daga cikin yunkurin ganin sasanci a jihar Kaduna tsakanin jama'ar da suka dade suna rikici a yankin Kudancin Kaduna.

Amma kuma, taron sasancin an shirya shi ne domin halartar mutum dari kacal daga yankin.

Hakazalika, shugabannin kungiyar kiristoci ta kasa reshen jihar Kaduna, sun ki halartar taron sasancin.

Shugaban kungiyar kiristoci ta kasa reshen kudancin Kaduna, Bishop Simon Peters Mutum, ya ce masu ruwa da tsaki a yankin sun ji labarin za a yi taro ne a lokacin da saura sa'o'i kadan a fara, The Punch ta wallafa.

Malamin addinin kiristan a wata takarda ya ce, "Mun so ace an sauya lokacin taron sasancin har sai an amsa mana tambayoyin da muke da su a kan yadda taron zai kasance."

Kashe-kashe: CAN da shugabannin kudancin Kaduna sun ki halartar taron sasanci
Kashe-kashe: CAN da shugabannin kudancin Kaduna sun ki halartar taron sasanci. Hoto daga The Punch
Asali: UGC

KU KARANTA: Karin kudin man fetur: 'Yan sanda sun ja kunnen mutanen dake shirin zanga-zanga a Borno

Hakazalika, SOKAPU, a wata wasika mai kwanan wata 6 ga watan Satumban 2020, ya sanar da kwamitin shirya taron cewa sun so tattaunawa da mashirya taron.

Wasikar ta samu saka hannun sakataren SOKAPU, Stephen Mallan, wacce ya tattauna a kan bukatar a sake gayyatar wani taron domin yin sasanci a kan rikicin kudancin Kaduna.

KU KARANTA: Karfin hali: Wani mutumi ya bindige matarshi har lahira a cikin ofishin 'yan sanda yayin da taje kai karar shi

A wata wasika da sakataren CAN na jihar, Rabaren Sunday Ibrahim ya mika ga shugaban masu shirya taron, Fasto James Wuye, ya ce kungiyarsu bata tabbatar da ingancin taron sasancin ba.

Wasikar ta ce, "CAN ba za ta goyi bayan dillalan rikici na jihar Kaduna ba wajen amfani da abinda ke faruwa domin cimma manufarsu. Kalubalen tsaro a kudancin Kaduna yana bukatar gagarumin shiri, ba na wasa ba.

"Kamar yadda yace, tun bayan da aka tsame CAN a cikin mashiryan taron sasancin, kawai aka gayyaceta daga baya, tabbas babu ingancin taron."

A wani labari na daban, Gwamna El-Rufai na jihar Kaduna ya ce ya san dalilin da yasa rikicin Kaduna ya ki ci balle cinyewa.

Ya ce wadansu malaman suna bukatar ambulan makare da kudi, hakan yasa rikicin ke ci gaba da karuwa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel