Yanzu-yanzu: Shahrarren dan bindigan da ya addabi jihar Benue, Gana, ya shiga hannu

Yanzu-yanzu: Shahrarren dan bindigan da ya addabi jihar Benue, Gana, ya shiga hannu

Shahrarren dan bindigan da aka dade ana nema ruwa a jallo, Terwase Agwaza Gana, ya mika wuya a jihar Benue.

Ya mika kansa ga kwamitin shirin afuwa a babbar filin kwallon Katsina ala dake karamar hukumar Katsina Ala a Arewacin jihar Benue ranar Talata, The Nation ta ruwaito.

Da dadewa an sanya kudi milyan goma ga duk wanda ya bayyana inda Gana yake boye a jihar amma ba'a samu wanda ya iya cin kudin ba.

Wannan shine karo na biyu da zai mika kansa ga hukumar bayan ajiye makamai da harsasai ga mambobin kwamitin afuwa da gwamnan Jihar, Samuel Ortom, ya shirya.

Amma daga baya yayi hannun riga da gwamnatin Samuel Ortom lokacin da yake jam'iyyar All Progressive Congress bayan sabanin da suka samu.

Gana, wanda ake zargi da laifin kisan hadimin gwamna Ortom kan lamuran tsaro, Denen Igbana, ya koma mabuyarsa a daji.

Ana kyautata zaton cewa shine ummul haba'isin ayyukan yan bindiga a yankin Sankera da ya tattari Ukun, Logo da karamar hukumar Katsina Ala.

A yanzu haka, an garzaya da Gana gidan gwamnatin jihar dake Makurdi inda gwamna Ortom ya karbeshi.

Yanzu-yanzu: Shahrarren dan bindigan da ya addabi jihar Benue, Gana, ya shiga hannu
Gana bindiga
Source: Twitter

A wani labarin daban,Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta bawa ƴan Najeriya na gari lasisin mallakar manyan bindigu kamar AK47 a matsayin matakin ƴaki da ƙallubalen tsaro a ƙasar.

Gwamnan ya ce a ɗauki tsauraran matakai da dokoki da suka dace domin hana safarar bindigun ta haramtattun hanya kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Wannan da wasu bukatun duk suna dauke ne cikin batutuwan da gwamnan ya gabatar a wani ƙasida da ya gabatar a ranar Talata yayin wani taron intanet da Cibiyar Shugabanci tare da hadin gwiwar NGF suka hada.

A cikin ƙasidar da ya gabatar, Ortom yace ya zama dole gwamnatoci a dukkan matakai su amince cewa rashin tsaro babban barazana ce ga cigaban kasar kuma su dage don dakile ta.

Ya kuma bayar da shawarar a rika bawa hukumomin tsaro isassun kudaden horaswa da zai taimaka musu wurin yaki da rashin tsaro a zamanance.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel