Yakamata masu fadi a ji a Najeriya su yi mana adalci - Buhari

Yakamata masu fadi a ji a Najeriya su yi mana adalci - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Tarata, ya ce yakamata masu kudin Najeriya su yi wa mulkinsa adalci, Channels TV ta wallafa.

Shugaban kasar ya bayyana hakan a yayin rufe taron duba ayyukan ministoci na shekarar farko wanda aka yi a Abuja.

"Ina son in yi kira ga masu hannu da shuni na Najeriya da su yi mana adalci," Buhari yace yayin da yake sanar da cewa mulkinsa ya yi kokari mai yawa duk da rashin kayan aiki.

Ya ce a kalla ana samar da danyen man fetur daga 1999 zuwa 2014, ganga miliyan 2.1 kuma ana siyar da ita a dala dari kowacce ganga.

Ya ce, "A lokacin da muka zo, ya fadi zuwa dala 37 ko 38 ganga daya. Sakamakon 'yan tawayen da aka yi fama da su a mulkin, ana samun ganga rabin miliyan a kowacce rana.

"Ina so ku dai duba, wanne hali ababen more rayuwa na kasar nan suke ciki duk da rashin samun kudi da ake yi. Tituna da dogo duk matattu ne, babu wutar lantarki. Ina kudin yake zuwa?"

Shugaban kasa ya ce yana iyakar kokarinsa wurin ganin ya yaki rashawa ta hanyar da ya dace ba ta yadda mulkin soja suke yi ba.

"Amma a halin yanzu ana kira na da baba go slow," yace.

Yakamata masu kudin Najeriya su yi mana adalci - Buhari
Yakamata masu kudin Najeriya su yi mana adalci - Buhari. Hoto daga Channels TV
Source: Twitter

KU KARANTA: Bidiyo: Yariman Dubai ya ajiyewa tsuntsaye wata sabuwar mota ta alfarma da za su dinga shakatawa a ciki

A wani labari na daban, Malam Garba Shehu, babban mai bai wa shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, shawara a fannin yada labarai, ya ce gwamnatocin da suka shude basu da karfin guiwar daukar matakan da suka dace.

A wata takardar da Shehu ya fitar a ranar Lahadi, ya ce za a tuna da shugaban kasa Muhammad Buhari ko nan gaba, a matsayin shugaban da ya bada "gudumawa ga habakar tattalin arziki da ci gaban kasar nan, tare da kawo karshen dukkan wata rashawa da ke tattare da tallafin man fetur."

A watan Maris da ta gabata, gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta sanar da cewa kamfanin man fetur na Najeriya ba zai ci gaba da saka wani banbanci tsakanin farashin da aka samu man fetur ba da kuma wanda za a siyar da shi.

KU KARANTA: Karfin hali: Wani mutumi ya bindige matarshi har lahira a cikin ofishin 'yan sanda yayin da taje kai karar shi

A saboda hakan, za a dinga duba farashin man fetur a kowanne wata domin ya zama daidai da yadda danyen man fetur yake a kasuwannin duniya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel