Faɗa a gidan yari: Fursuna ya datse yatsun gandireba ya haɗiye a Italy

Faɗa a gidan yari: Fursuna ya datse yatsun gandireba ya haɗiye a Italy

Wani shugaban kungiyar miyagu da aka yi wa ɗaurin rai da rai a gidan yari ya gutsure yatsun gandireba ya haɗiye yayin faɗa kamar yadda wata kafar watsa labarai na Italiya ta ruwaito.

Guiseppa Fanara mai shekaru 60 da aka yi wa ɗaurin rai da rai a gidan yarin Rebibbia a ƙasar Rome ya kai wa masu gadin gidan yari bakwai hari a watan Yuni da suka shigo dakinsa yin bincike kamar yadda Daily Il Messagero ta ruwaito.

A halin yanzu Fanara wadda ɗan kungiyar Mafiya ta Cosa Nostra ne yana shekararsa ta tara kenan a gidan yarin na ƙasar Italiya.

Faɗa a gidan yari: Fursuna ya datse yatsun gandireba ya haɗiye
Faɗa a gidan yari: Fursuna ya datse yatsun gandireba ya haɗiye. Hoto daga The Punch
Source: Twitter

KU KARANTA: Mutum biyu sun riga mu gidan gaskiya sakamakon harin da ƴan IPOB suka kai wa hausawa a Rivers

Saboda hatsarin da ke tattare da mutane irinsa, a kan ware su daban ne a gidan yarin a basu ɗaki su kadai domin hana su cigaba da aikata laifuka daga cikin gidan yarin inda suka hulda da sauran fursunoni.

"Yayin fadar da suka yi, Fanara ya yi amfani da haƙoransa ya guntule ƙaramin yatsan gandireban na hannun dama," a cewar jaridar.

"Sai dai an kasa gano ɗan yatsar hakan yasa wani mai bincike a kasar ta Rome ya cimma matsayar cewa an haɗiye yatsar ne," jaridar ta kara da cewa.

Daga nan sai Fanara ya yi wa sauran masu gadin gidan yarin shida barazana da tsinke da ya ke rike a hannunsa inda ya ce, "zan yanka wuyan ku kamar aladai!"

DUBA WANNAN: Hotuna: Ƙaramin yaron da al'umma suka bawa tallafin kuɗi ya buɗe 'katafaren kanti' a Kano

Tuni dai mayar da Fanara wani gidan yarin a mai tsauraran matakan tsaro a Sardina inda ake tuhumar sa da sabbin laifuka da suka hada da faɗa da rashin yarda a kama shi.

A farkon wannan shekarar kasar Italy ta yi niyyar sakin wasu tsaffin shugabannin kungiyar miyagu ciki har da ƴan Cosa Nostra.

Amma al'ummar ƙasar sun nuna ƙin amincewarsu hakan dole ma'aikatar Shari'a kasar ta dakata da batun ta ce za ta sake bita.

A wani rahoton, kun ji cewa a ƙalla hausawa 2 mazauna Oyigbo a ƙaramar hukumar Oyigbo ta jihar Rivers ne suka mutu sakamakon harin da wasu da ake zargin ƴan kungiyar masu fafutikan kafa ƙasar Biafra, IPOB, suka kai musu a Oyigbo.

Wani ganau ya bayyana cewa fusatattun mambobin na ƙungiyar IPOB sun kai wa Hausawa mazauna Oyigbo hari a ranakun Asabar da Lahadi.

Ganau ɗin ya ce an kashe aƙalla mutane biyu yayin da wasu da dama sun samu munannan raunuka kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel