Kakar wasanni ta Premier: Matasan 'yan wasa biyar masu tashe a taka leda

Kakar wasanni ta Premier: Matasan 'yan wasa biyar masu tashe a taka leda

A ranar Asabar ne aka shirya fara kakar wasanni ta Premier ta wannan shekarar, tare da wasu matasan 'yan wasa, da su ka fara tashe a wasan na taka leda.

Bayan da dan wasan Manchester United Mason Greenwood ya zamo dan wasa mai tashe a kakar bara, jaridar AFP Sport ta duba wasu 'yan wasa biyar da za su yi tashe a kakar wasan bana.

Phil Foden (Manchester City)

Ana masa kirari da dan wasa mai baiwa a kungiyar kwallon da ta lashe kofin duniya na rukunin 'yan shekaru 17 a shekaru uku da suka wuce, akwai hasashen zai tsere sa'a a kakar wasan bana.

Barin David Silva Manchester City, ya bar babban gibi a tawagar kocin kungiyar Pep Guadiola, wanda ake sa ran Foden zai cike wannan gibi.

KARANTA WANNAN: Pakistan ta yankewa wani Kirista hukuncin kisa saboda aika sakon batanci ga Musulmi

Phil Foden (Manchester City)
Phil Foden (Manchester City)
Source: Twitter

Guardiola ya fara nuna yardarsa akan dan wasan mai shekaru 20, lokacin da ya sanya shi a wasan karshe na kakar bara tsakaninsu da Aston Villa, inda kuma ya zamo zakaran wasan, kuma ya ba kungiyar nasara kan Real Madrid a kofin zakarun nahiyar turai.

Kalvin Phillips (Leeds)

Shekaru biyu da fara taka leda, dan wasa Phillips ya farantawa kungiyar kwallon kafa ta Leeds rai, ta hanyar basu nasarar komawa kakar wasan Premier.

A shekaru biyu da suka gabata, ana kallon kamar dan wasan ba zai tabuka komai ba, amma zuwan Marcelo Bielsa a matsayin kocin Leed a 2018, ya canja tarihin dan wasan.

Bielsa ne ya fahimci cewa Phillips ya fi taka leda da kyau idan yana buga wasan gaba, mai makon wasan kato bayan kato da ya saba bugawa a baya.

KARANTA WANNAN: Ta sa hakori ta gutsirewa mijinta mazakuta saboda ya gaza kashe bera a dakinta

Tun bayan samun wannan canji, dan wasan mai shekaru 24 ya farfado daga doguwar sumar da ya yi, har ya zamo dan wasa mai daraja a kun kungiyar kwallon kafa ta Leeds.

Kalvin Phillips (Leeds)
Kalvin Phillips (Leeds)
Source: Twitter

Bukayo Saka (Arsenal)

Biyo bayan rawar da ya taka a wasannin 2019/20, Bukayo Saka mai shekaru 19, ya samu karramawa ta kambun matashin dan wasa a PFA na wannan shekarar.

Kasancewarsa mai baiwar buga wasa da kafar dama ko hagu, a wasan gaba da baya, kai harma da tsakiya, Saka ya nuna bajintarsa lokacin da Arsenal ta samu nasara kan Liverpool a kambun Community Shield.

Dan wasan Manchester City, Kevin De Bruyne da na Liverpool Trent Alexander-Arnold ne kawai suka fi Saka bayar da kwallayen da aka ci a kakar Premier, tun daga aka fara kakar bara.

Bukayo Saka (Arsenal)
Bukayo Saka (Arsenal)
Source: Twitter

Matheus Pereira (West Bromwich Albion)

Dan wasan mai shekaru 24 dan kasar Brazil, ya kasance zakaran gwajin dafi a kungiyar Albion a kakar wasannin bara.

A kakar wasansa ta farko a taka leda a kasar turai, masu tsaron gida sun gagara gano lagon Pereira, inda har dan wasan ya zura kwallaye 8 a raga, da kuma bada tallafin kwallaye 16.

Da farko ya je Albion ne a matsayin haya daga kungiyar Sporting Lisbon, amma Albion ta sayi dan wasan akan $12m, la'akari da kwarewarsa wajen taka leda.

Matheus Pereira (West Bromwich Albion)
Matheus Pereira (West Bromwich Albion)
Source: Twitter

Curtis Jones (Liverpool)

Jones ya nuna tsantsar kwarewarsa a yayin da ya zura kwallo a ragar Everton a kakar wasan kofin FA na bara, a wasan na kusa da na kusa da na kare, inda ya ci kwallon daga tsakiyar fili.

Kwazon dan wasan tsakiyar mai shekaru 19 da kuma hikimarsa, ya sa ya zamo tauraro, kuma abun kwatance a wajen kocin Liverpool Jurgen Klopp.

Sau 8 yana buga wasa tun bayan da ya nuna bajintarsa a wasansu da Everton, kuma a watan da ya gabata ne ya samu 'yanci daga zama a teburin canji a kambun wasanni na Community Shield.

A yayin da Klopp ke kaffa kaffar sayen 'yan wasa da kuma yakininsa akan samun matasa a Liverpool, Jones na da damar buga wasanni a kakar Priemer bana.

Curtis Jones (Liverpool)
Curtis Jones (Liverpool)
Source: Twitter

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel