Buhari: Abinda na sanar da Trump a yayin da ya zargeni da kashe Kiristoci

Buhari: Abinda na sanar da Trump a yayin da ya zargeni da kashe Kiristoci

A ranar Talata, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana martanin da yayi wa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, a kan zarginsa da yayi da kashe Kiristoci.

A ranar 30 ga watan Afirilun 2018, Buhari ya gana da Trump a birnin Washington domin tattaunawa a kan ta'addancin Boko Haram, tattalin arziki da sauransu.

A jawabinsa na taron da yayi da ministoci a fadarsa da ke Abuja a yau Talata, Buhari ya ce ya sanar da takwaransa na kasar Amurka cewa rikicin makiyaya da manoma ba na addini bane.

"A gaskiya ni ne kadai shugaban kasa daga cikin kasahen Afrika da shugaban kasar Amurka ya gayyata.

"Kuma a lokacin da nake ofishinsa daga ni sai shi, ya dubeni a cikin ido inda ya tambayeni dalilin da yasa nake kashe Kiristoci," Buhari yace.

“A take na sanar da shi cewa rikicin da ke tsakanin makiyaya da manoma ya dade a Najeriya. Ya girmeni ballantana shi. Ina tunanin na bashi wasu shekaru.

"Da sauyin yanayi tare da karuwar yawan jama'a hadi da al'adun makiyaya, idan kana da shanu 50 suna kiwo, duk inda kaje suna biye. Basu damu da gonar waye ba," ya kara da cewa.

Buhari: Abinda na sanar da Trump a yayin da ya zargeni da kashe Kiristoci
Buhari: Abinda na sanar da Trump a yayin da ya zargeni da kashe Kiristoci. Hoto daga The Cable
Source: Twitter

KU KARANTA: Babu kasar da ta kai Najeriya arhar man fetur a Afrika har yanzu - Lai Mohammed

Har ila yau, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Tarata, ya ce yakamata masu kudin Najeriya su yi wa mulkinsa adalci, Channels TV ta wallafa.

Shugaban kasar ya bayyana hakan a yayin rufe taron duba ayyukan ministoci na shekarar farko wanda aka yi a Abuja.

"Ina son in yi kira ga masu hannu da shuni na Najeriya da su yi mana adalci," Buhari yace yayin da yake sanar da cewa mulkinsa ya yi kokari mai yawa duk da rashin kayan aiki.

KU KARANTA: Babu kasar da ta kai Najeriya arhar man fetur a Afrika har yanzu - Lai Mohammed

Ya ce a kalla ana samar da danyen man fetur daga 1999 zuwa 2014, ganga miliyan 2.1 kuma ana siyar da ita a dala dari kowacce ganga.

Ya ce, "A lokacin da muka zo, ya fadi zuwa dala 37 ko 38 ganga daya. Sakamakon 'yan tawayen da aka yi fama da su a mulkin, ana samun ganga rabin miliyan a kowacce rana.

"Ina so ku dai duba, wanne hali ababen more rayuwa na kasar nan suke ciki duk da rashin samun kudi da ake yi. Tituna da dogo duk matattu ne, babu wutar lantarki. Ina kudin yake zuwa?"

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel