Wata sabuwa: Daga yanzu babu ruwanmu da farashin man fetur - FG

Wata sabuwa: Daga yanzu babu ruwanmu da farashin man fetur - FG

PPRA, hukumar gwamnatin tarayya da ke da alhakin kayyade farashin albarkatun man fetur, ta ce daga yanzu babu ruwanta da maganar tsayar da farashin mai, magana ta koma hannun 'yan kasuwa.

Jaridar Punch ta rawaito cewa babban sakataren hukumar PPRA, Abdulkadir Saidu, ne ya sanar da hakan.

A cewar jaridar Punch, Saidu ya bayyana cewa daga yanzu kayyade farashin litar mai zai dogara ne a kan bukatarsa da kuma farashin danyen mai a kauwar duniya.

Hakan na nufin gwamnati ta tsame hannunta daga tsayarwa ko kayyade farashin litar mai.

Saidu, wanda babban manaja a PPRA, Victor Shidok, ya wakilta, ya ce PPRA za ta cigaba da sa-ido a kan yadda 'yan kasuwa ke sayar da man fetur domin tabbatar da cewa ba a zalunci jama'a ba.

"Alhakinmu ne mu tabbatar da cewa mun kare hakkin jama'ar da ke sayen man fetur domin amfaninsu," a cewar Saidu.

A cewar Saidu, har yanzu 'yan kasuwa basu fara shigo da tataccen man fetur ba saboda karancin kudaden kasashen waje a kasuwar canjin kudade.

An gaza cimma matsaya a tsakanin 'yan kasuwa da hukumar NNPC a kan tsayar da farashin litar mai a gidajen mai mallakar 'yan kasuwa.

Kungiyar dillalan man fetur ta sha bayyana cewa ba zata iya sayar da litar man fetur a kan farashin da gwamnati ta tsayar ba.

Wata sabuwa: Daga yanzu babu ruwanmu da farashin man fetur - FG
Wata sabuwa: Daga yanzu babu ruwanmu da farashin man fetur - FG
Source: UGC

'Yan kasuwar na kafa hujja da cewa zasu yi asara matukar suka sayar da litar mai a kan farashin da gwamnati ta saka saboda suna kashe kudin dakon mai zuwa gidajensu na mai.

A makon jiya ne gwamnatin tarayya ta sanar da kara farashin litar man fetur, lamarin da ya harzuka 'yan najeriya da dama.

KARANTA: Cigaba: Ganduje ya saka na'urorin sa-ido a manyan titunan Kano, bidiyon yadda suke aiki

KARANTA: Tura ta kai bango: 'Yan Najeriya sun harzuka, sun mayarwa Buhari martani

Kungiyar daliban Najeriya (NANS) ta fadawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya janye karin farashin man fetur da gwamnatinsa ta yi ko kuma dalibai su mamaye titunan Najeriya a wata gagarumar zanga-zanga da bai taba ganin irinta ba.

NANS ta ce ta yi matukar girgiza da jin labarin cewa gwamnati ta sanar da yin karin kudin litar man fetur daga N145 zuwa N161.

A cikin wani jawabi da mataimakin shugaban kungiyar, Kwamred Ojo Raymond, ya fitar, NANS ta bayyana karin farashin man fetur a matsayin almara, tunzura jama'a da kuma nuna zallar rashin tausayi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel