Hotuna: Ma'aikatan da suka yi murabus sun hana shiga da fita a gidan gwamnatin Delta

Hotuna: Ma'aikatan da suka yi murabus sun hana shiga da fita a gidan gwamnatin Delta

Tsoffin malaman makarantun firamare tare da na kananan hukumomi a jihar Delta da suka yi murabus, sun fito zanga-zanga a ranar Talata.

Sun mamaye kofar gidan shiga gwamnatin jihar inda suke bukatar a biya su hakkokinsu wanda gwamnatin Gwamna Ifeanyi Okowa ta hanasu.

Masu zanga-zangar rike da takardu dauke da bayanai sun hana shige da fice a gidan gwamnatin. Sun hana dukkan jami'an gwamnati da masu ziyara shiga gidan.

Da duminsa: Ma'aikatan da suka yi murabus sun hana shiga da fita a gidan gwamnatin Delta
Da duminsa: Ma'aikatan da suka yi murabus sun hana shiga da fita a gidan gwamnatin Delta. Hoto daga SaharaReporters
Source: Twitter

KU KARANTA: Sau 1 nayi lalata da ita, ba sau 4 bane - Tsohon da yayi wa yarinya fyade

Da duminsa: Ma'aikatan da suka yi murabus sun hana shiga da fita a gidan gwamnatin Delta
Da duminsa: Ma'aikatan da suka yi murabus sun hana shiga da fita a gidan gwamnatin Delta. Hoto daga SaharaReporters
Source: Twitter

KU KARANTA: Dalilin da yasa gwamnatin tarayya ta cire tallafin man fetur - Fadar shugaban kasa

Da duminsa: Ma'aikatan da suka yi murabus sun hana shiga da fita a gidan gwamnatin Delta
Da duminsa: Ma'aikatan da suka yi murabus sun hana shiga da fita a gidan gwamnatin Delta. Hoto daga SaharaReporters
Source: Twitter

Sun zargi gwamnan jihar da nuna musu halayyar mugunta a kan yadda yayi shiru ya hana su hakkokinsu.

Kamar yadda masu ritayar suka bayyana dauke da kayayyakin girki, tabarma da sauran kayayyakin, sun ce da gangan Gwamna Okowa ya hana su kudadensu tun bayan da ya hau kujerarsa.

A lokacin rubuta wannan rahoton, masu zanga-zangar suna wakoki inda suke bukatar hakkokinsu.

Wasu kuwa sun baza tabarminsu a gaban kofar shiga gidan gwamnatin yayin da jami'an tsaro suka hana su shiga.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel