A gaban 'ya'yana yake dukana kamar jaka - Matar aure ta sanar da alkali

A gaban 'ya'yana yake dukana kamar jaka - Matar aure ta sanar da alkali

Wata matar aure mai suna Ladidi Abbas, a ranar Talata ta maka mijinta mai suna Shehu Abbas a gaban wata kotun shari'ar Musulunci da ke zama a Magajin Gari, a Kaduna.

Ladidi ta bukaci mijinta da ya sauwake mata igiyoyin aurensa, saboda dukan da take sha a hannunsa a duk lokacin da suka samu matsala, jaridar The Nation ta wallafa.

Kamar yadda tace, an kwantar da ita a asibiti na tsawon kwanaki 13 a wancan dukan da yayi mata.

"Ya saba dukana a gaban 'ya'yana, wancan karon da ya dukeni sai da aka kwantar da ni a asibiti na tsawon kwanaki 13," Abbas yace.

Ta mika bukata gaban kotun da cewa a tsinke igiyoyin aurensu kuma a bata rikon 'ya'yanta.

Wanda ake kara, Abbas, dan jarida ne da yayi murabus kuma yana zama a Rigasa. Ya musanta dukkan zargin da ake masa.

"A yanzu ne nafi jin kaunar matata," yace, tare da rokon kotun da ta bashi lokaci domin shawo kan matasalar aurensu.

Alkalin kotun, Murtala Nasir, bayan sauraron dukkansu, ya bada umarni ga mai karar da ta kawo shaidun ikirarin da tayi.

Ya dage sauraron karar zuwa ranar 10 ga watan Satumban 2020 domin ci gaba da shari'a.

A gaban 'ya'yana yake dukana kamar jaka - Matar aure ta sanar da alkali
A gaban 'ya'yana yake dukana kamar jaka - Matar aure ta sanar da alkali. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kashe mutum 10, sun yi garkuwa da manoma

A wani labari na daban, wata mata mai suna Blessing Amuson a ranar Talata ta sanar da wata kotun gargajiya da ke zama a Ile-Tuntun a jihar Ibadan cewa ta tsinke aurensu mai shekaru uku.

Matar auren ta bukaci rabuwa da mijinta mai suna Babatunde sakamakon tsawwala mata da sirikinta yayi wanda tace yana kokarin lalata musu aure.

A yayin bayani a gaban alkali, Amuson , wacce ke zama a yankin Apata da ke Ibadan, ta ce: "Sirikina ne ke son kashe min aure da yadda yake gurbata tunanin mijina.

"Kafin aurena da Babatunde, na samu aiki mai kyau da gwamnatin jihar Legas kuma mun yi yarjejeniya cewa zan cigaba da aiki bayan aurenmu.

"Amma kuma, bayan auren ya canza kuma ya bukaci in ajiye aikina domin in dawo Ibadan.

"Sau da yawa, yana zuwa wurin iyayensa kuma a nan yake canza tunaninsa. Daga baya ya koreni daga gidansa."

KU KARANTA: FG ba za ta iya cigaba da kashe N5bn a kowanne wata ba a kan 'yan gudun hijira - Majalisa

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel