Wata mata mai shekaru 31 ta fada dam ta mutu yayin daukan hotuna

Wata mata mai shekaru 31 ta fada dam ta mutu yayin daukan hotuna

Wata mata ta zame ta faɗa cikin dam a lokacin da ta ke ɗaukan hotuna yayin wata liyafar cin abinci na masoya da aka yi a Chepkiit Waterfalls da ke yankin Nandi.

Ruwa ya yi awon gaba da Dorcas Jepkemoi Chumba mai shekaru 31 a ranar Lahadi yayin da saurayinta Banjamin Kazungu ke amfani da wayan ta yana ɗaukan ta hoto.

Iyalan Miss Chumba da suka fito daga kauyen Kapchorwa a Keiyo ta Kudu sun tare a Chepkiit Waterfalls tun ranar Lahadi da nufin za a gano gawarta.

Wata mata mai shekaru 31 ta fada dam ta mutu yayin daukan hotuna
Wata mata mai shekaru 31 ta fada dam ta mutu yayin daukan hotuna
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Kudancin Kaduna: Mabiya sun ce fasto ya siyo bindigu da kudin baikonsu

Masunta a yankin da ke neman gawar ta ba suyi nasara ba a lokacin da ake haɗa wannan rahoton kamar yadda da Nation ta ruwaito.

Ɗan uwan ta Victor Kiptoo ya roki gwamnatin Uasin Gishu da Nandi su taimake su wurin gano gawar ta.

"Abin ya faru kuma mun rungumi ƙaddara, roƙo kawai muke yi a taimake mu a gano gawar ta," in ji shi.

Shugaban ƴan sanda na yankin Nandi, Samson Ole Kina ya ce ambaliyar ruwa ce ke kawo cikas wurin gano gawar.

KU KARANTA: Ambaliyar ruwa: Mutum 20 sun mutu, gidaje da gonaki 50,000 sun salwanta a Jigawa

Ya bukaci iyalan wacce ta rasun su ƙara haƙuri yayin da jami'an da ke aikin za su cigaba da nazarin lamarin.

"Dam ɗin ya zama wuri mai hatsari musamman a lokacin damina, ana shawartar mutane su dena zuwa wurin don tsare lafiyar su," in ji shi.

Ƙoƙarin da Mista Kazungu ya yi na ceto masoyiyarsa bai cimma nasara ba duba da irin karfin ruwa wadda dole haka ya yi ta kallon sahibarsa ruwa na tafiya da ita.

"Na yi ƙoƙarin ceto ta amma banyi nasara ba duba da cewa dam ɗin ya cika maƙil," a cewarsa bayan afkuwar mummunan lamarin.

A yanzu, Mista Kazungu ya ce abinda zai rika amfani da shi wurin tunawa da ita shine hoton ta da ya ɗauka kafin ta faɗa cikin ruwan.

A wani labarin daban, kun ji mutane huɗu ƴan gida ɗaya sun mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a hanyan Kano zuwa Jigawa a ranar Asabar.

Wani ɗan uwan wadanda suka rasu, Shehu Yusuf Kazaure ya ce dukkan wadanda suka mutu ƴan gidan Hajiya Safiya Mohammed ce, direktan Ilimin gaba da sakandare a ma'aikatar Ilimi na jihar.

Suna kan hanyarsu ta zuwa ƙaramar hukumar Malam Madori ne ɗaurin aure yayin da motarsu ta yi Kundin bala a kusa da Danladin-Gumel a ƙaramar hukumar Gumel.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel