Buhari ya yi magana a kan ƙarin kudaden lantarki da man fetur

Buhari ya yi magana a kan ƙarin kudaden lantarki da man fetur

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya ce gwamnati ba za ta mayar da tallafin kuɗin man fetur ba ma'ana janye tallafin ya zauna daram dam kenan.

Buhari ya kuma ce ƙarin kuɗin wutar lantarki da kamfanonin rabar da wutar lantarki, DisCos suka yi ya zama dole ne duk da cewa abin ya dame shi kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce gwamnati na iya ƙoƙarin ta domin rage raɗaɗin da ƙarin zai yi a rayuwar al'umma a lokaci guda kuma yana ƙoƙarin ceto tattalin arzikin ƙasar daga ruguje wa.

Buhari ya yi magana a kan ƙarin kudaden lantarki da man fetur
Buhari ya yi magana a kan ƙarin kudaden lantarki da man fetur. Hoto daga Daily Trust
Source: Twitter

Shugaban ƙasar ya ce kamar sauran ƴan Najeriya, baya farin ciki da irin lantarkin da DisCos ɗin ke rabar wa duk da cewa akwai wasu matsaloli da suke fuskanta.

DUBA WANNAN: Hotuna: Ƙaramin yaron da al'umma suka bawa tallafin kuɗi ya buɗe 'katafaren kanti' a Kano

Buhari ya yi wannan jawabin ne yayin taron kwanaki biyu da aka gudanar na bita kan ayyukan ministoci da aka yi a Abuja inda mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo ya wakilce shi.

Duk da rashin daɗinsa, Buhari ya ce annobar COVID-19 wadda ta shafi tattalin arzikin ƙasashen duniya da dama ce ta saka gwamnatinsa ɗaukan wasu matakai da ake fatan za su amfani ƙasar a nan gaba.

Buhari ya fadi wasu matsalolin da cigaba da biyan tallafin man fetur ɗin ka iya haifarwa kuma ya ce idan aka mayar da shi za a fara samun dogayen layukan man fetur a gidajen mai.

Ga wani sashi cikin abinda ya ce: "Kamar yadda ku ka sani farashin man fetur ya faɗi a lokacin kulle na korona, gwamnati ta cire hannun ta a batun dai-daita farashin man fetur domin masu saya su samu sauƙi a duk lokacin da farashin ya yi sauki kuma anyi maraba da hakan.

"Abu mai hatsari na biyu kuma shine yiwuwar dawowar layyukan man fetur - wadda ya zama tarihi a wannan gwamnatin. Yanzu ƴan Najeriya ba su yin layi a gidajen mai don sayan man fetur wasu lokutan da tsada sosai. Kamar yadda na faɗa a baya, an cire batun biyan tallafin man fetur domin kasar ba za ta iya cigaba da biya ba idan har ana son samun kudaden da za a inganta wasu ɓangarori kamar ilimi, kiwon lafiya da sauran bangarorin more rayuwa. Ba mu da zaɓi ne yanzu.

"Duk da haka ina son tabbatar wa ƴan Najeriya cewa gwamnati ba za ta saka idanu ta bari ƴan kasuwa su rika ƙara kuɗi ba bisa ƙa'ida ba. Gwamnatin za ta rika sa ido ta hanyar amfani da Hukumar Kula da Farashin Man Fetur (PPPRA).

"Hakan ne yasa kwanakin baya PPPRA ta ƙayyade farashin da ƴan kasuwa za su rika sayar da man fetur. Wani abin alheri kuma shine kowa na iya shigo da man fetur domin sayarwa kuma hakan na iya tilastawa ƴan kasuwa karya farashin mai," in ji shi.

Da ya ke magana a kan ƙarin kuɗin lantarki, Buhari ya ce bai gamsu da irin wutar da DisCos ke bawa ƴan Najeriya ba.

KU KARANTA: Sun mayar da mu karuwai, ga horo da yunwa: Yar Najeriya da aka ceto daga Libya

Sakamakon hakan, shugaban kasar ya ce gwamnatinsa na ƙoƙarin ganin an samar wa aƙalla ƴan Najeriya miliyan 5 mita.

Ya ce gwamnatinsa za ta cigaba da kare talakawa da gajiyayyu a yayin da ta ke ganin an inganta samar da lantarkin ga ƴan Najeriya.

Buhari ya kuma ce gwamnati za ta samar wa ƴan Najeriya kimanin miliyan biyar lantarki da hanyar hasken rana wato solar cikin watanni 12 masu zuwa ga wadanda lantarki bai kai gare su ba.

A wani rahoton, kun ji cewa Ƴan Najeriya da kungiyoyi da dama sun soki ƙarin kuɗin wutar lantarkin da na man fetur inda wasu ke kiraye-kirayen cewa a gudanar da zanga-zangar nuna ƙin amincewa da batun.

Babban jami'yyar hamayya a ƙasar, PDP da ƙungiyar ƴan kabilar Yarabawa ta Afenifere suna daga cikin wadanda suka soki ƙarin kuma suka shawarci ƴan Najeriya su fito su nuna rashin amincewarsu da batun.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel