Sulhu alkhairi ne: Yan bindigan Sokoto sun mika wuya, su sake mutane 8 da suka sace

Sulhu alkhairi ne: Yan bindigan Sokoto sun mika wuya, su sake mutane 8 da suka sace

Kasurguman yan bindigan da suka addabi gabashin jihar Sokoto, Arewa maso yammacin Najeriya sun ajiye makaman yaki sakamakon zaman sulhu da gwamnatin jihar ta shirya.

Kwamishanan harkokin tsaron jihar, Kanal Garba Moyi (Mai Ritaya), ya ce kimanin yan bindiga 200 suka ajiye makamansu kuma suka mika wuta.

Hakazalika an tattaro cewa yan bindigan sun saki mutane takwas da suka sace, kuma sun mikawa gwamnatin jihar dabbobin da suka sace, Rahoton Daily Trust.

A cewar kwamishinan, Kanal Garba Moyi (Mai Murabus), yace an samu dabbobi 500 daga hannunsu., Sahara Reporters ta ruwaito.

Kanal Moyi ya yi bayanin cewa an samu nasarar yarjejeniya da yan bindigan ne, kuma daga yanzu ba zasu sake garkuwa da wani ba, yayinda gwamnati kuma ba zata kama wani cikinsu ba sai dai idan an ga mutum da makamai.

Game da yan bindigan da suka ajiye makamansu kuma suka koma noma da kiwo, kwamishanan ya ce gwamnatin jihar na taimaka musu da abincin dabbobi da kayayyakin noma.

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta bada kwangilan gina 'Dam' a Kamarawa sakamakon nasarar da aka samu na yin sulhu.

"Da tuni an kaddamar da ginin, amma an gaza saboda hare-hare da ambaliya." Yace

"Muna shirin gina filayen kiwo da makarantu domin ilmantar da yaransu,"

Kwamishanan ya jaddada cewa wadanda ke sukan wannan sulhu da gwamnatin jihar tayi, suna hakan ne don babu wani dan 'uwansu da aka kashe ko aka sace.

Sulhu alkhairi ne: Yan bindigan Sokoto sun mika wuya, su sake mutane 8 da suka sace
Sulhu alkhairi ne: Yan bindigan Sokoto sun mika wuya, su sake mutane 8 da suka sace
Source: Twitter

KU KARANTA: Boko Haram ta kashe mutum huɗu yayin da suke barci, ta ƙona wasu uku da ransu a Borno

Hare-haren 'yan bindiga a garin Sokoto yayi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane, yayinda da dama sun jikkata.

Wata kungiyar 'yan jihar Sokoto ta yi kiran gaggawa ga gwamnati a kan ta dauki mataki da wuri.

Kungiyar ta bayyana cewa, daga watan Janairun da ya gabata, an rasa a kalla rayuka 270 a jihar sakamakon hare-hare 20 da 'yan bindiga suka kai jihar.

A yayin jawabi ga manema labarai a madadin kungiyar, Farfesa Nasiru Gatawa ya ce suna cikin matsanancin hali don haka suna bukatar gwamnati ta dauka matakan gaggawa.

Kamar yadda yace, "muna da kananan hukumomi 8 a yankin gabashin jihar. Sun hada da: Gada, Goronyo, Gwadabawa, Illeila, Issa, Rabbah, Sabon Birni da Wurno.

"Yankin da aka fi takura wa shine Sabon Birni. 'Yan bindigar na kai kawo yadda suke so da rana tsaka ba tare da wani yunkurin hana su ba daga gwamnati.

"Kowacce daga cikin kananan hukumomin na karkashin 'yan ta'adda don sun gurgunta tattalin arzikinsu tare da asarantar da rayuka da kadarori," yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel