Babu kasar da ta kai Najeriya arhar man fetur a Afrika har yanzu - Lai Mohammed

Babu kasar da ta kai Najeriya arhar man fetur a Afrika har yanzu - Lai Mohammed

Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed, ya bayyana cewa farashin fetur a Najeriya har a yanzu shine mafi karanta a kasashen yammaci da tsakiyar Afrika.

Idan za mu tuna, a ranar 1 ga watan Satumban 2020, gwamnatin tarayya ta kara farashin man fetur zuwa N162 a duk lita daya.

Ministan ya bayyana hakan a yayin jawabi ga manema labarai na hadin guiwa wanda ministan wutar lantarki, Saleh Mamman da karamin ministan man fetur, Timipre Sylva suka hada.

Mohammed ya ce , duk da halin da tattalin arzikin kasar nan ke ciki, gwamnati ta ci gaba da aiwatar da manyan ayyukanta ballantana biyan albashi. Amma kuma dole ne ta cire wa kanta al'adun da za su durkusar mata da tattalin arzikinta.

"Gwamnati ba za ta iya bada tallafin man fetur ba saboda bata ganin daidai a hakan. Yawaita neman man fetur yanzu ya zama tarihi.

"Lokutan da 'yan Najeriya ke daukar tsawon sa'o'i suna jiran layi ya zo kansu ko kwanaki domin siyan man fetur duk ya wuce.

"Tabbas ko a kasafin kudin 2020 da aka sake bitarsa babu tallafin man fetur saboda ba za mu iya biya ba," yace.

Ministan ya bayyana cewa, daga 2006 zuwa 2019, tallafin man fetur kadai ya lashe N10.413 tiriliyan kuma a duk shekara yana lashe N753.8 biliyan.

Babu kasar da ta kai Najeriya arhar man fetur a Afrika har yanzu - Lai Mohammed
Babu kasar da ta kai Najeriya arhar man fetur a Afrika har yanzu - Lai Mohammed. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: FG ba za ta iya cigaba da kashe N5bn a kowanne wata ba a kan 'yan gudun hijira - Majalisa

Ya ce matatar man fetur ta kasa ta bayyana cewa, an fitar da tallafin man fetur har N257 biliyan a 2006, N272 biliyan a 2007, N631 biliyan a 2008, N469 biliyan a 2009, N667 biliyan a 2010, N2.105 tiriliyan a 2011 da N1.355 tiriliyan a 2012.

Ya kara da cewa, tallafin man fetur ya lamushe N1.316 tiriliyan a 2013, N1.217 tiriliyan a 2014, N654 biliyan a 2015, N144.3 biliyan a 2017, N730.86 a 2018 da N595 biliyan a 2019.

KU KARANTA: Najeriya ta yi rashi, babban basarake a Katsina ya rasu

Mohammed ya kara da cewa, zamanin tallafin man fetur ya zo karshe a watan Maris na 2020 bayan sanarwar hukumar daidaita farashin kayayyakin man fetur.

Ya tunatar da cewa, PPPRA ta sanar da cewa za a dinga daidaita farashin kayayyakin man fetur kamar yadda kasuwarsa ta duniya ta zo a lokacin.

A wani ci gaba makamancin hakan, Malam Garba Shehu, babban mai bai wa shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, shawara a fannin yada labarai, ya ce gwamnatocin da suka shude basu da karfin guiwar daukar matakan da suka dace.

A wata takardar da Shehu ya fitar a ranar Lahadi, ya ce za a tuna da shugaban kasa Muhammad Buhari ko nan gaba, a matsayin shugaban da ya bada "gudumawa ga habakar tattalin arziki da ci gaban kasar nan, tare da kawo karshen dukkan wata rashawa da ke tattare da tallafin man fetur."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel