Mutum biyu sun riga mu gidan gaskiya sakamakon harin da ƴan IPOB suka kai wa hausawa a Rivers

Mutum biyu sun riga mu gidan gaskiya sakamakon harin da ƴan IPOB suka kai wa hausawa a Rivers

A ƙalla hausawa biyu mazauna Oyigbo a ƙaramar hukumar Oyigbo ta jihar Rivers ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon harin da wasu da ake zargin ƴan kungiyar masu fafutikan kafa ƙasar Biafra, IPOB, suka kai musu a Oyigbo.

Wani ganau ya bayyana cewa fusatattun mambobin na ƙungiyar IPOB sun kai wa Hausawa mazauna Oyigbo hari a ranakun Asabar da Lahadi.

Ganau ɗin ya ce an kashe aƙalla mutane biyu yayin da wasu da dama sun samu munannan raunuka kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Mutum biyu sun riga mu gidan gaskiya sakamakon harin da ƴan IPOB suka kai wa hausawa a Rivers
Mutum biyu sun riga mu gidan gaskiya sakamakon harin da ƴan IPOB suka kai wa hausawa a Rivers. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

"Ranar Asabar aka fara kai harin sannan aka cigaba zuwa Lahadi. Wasu matasa da ake zargin ƴan IPOB ne sun kai hari wata unguwa da Hausawa suka fi yawa dauƙe da miyagun makamai. Mutum biyu sun mutu yayin da wasu sun jikkata," in ji shi.

KU KARANTA: Hotuna: Ƙaramin yaron da al'umma suka bawa tallafin kuɗi ya buɗe 'katafaren kanti' a Kano

Mai magana da yawun hausawa a jihar Rivers, Alhaji Musa Saidu ya yi Allah wadai da harin yayin da ya ke tabbatar wa majiyar Legit.ng Hausa afkuwar lamarin.

Alhaji Musa Saidu ya ce wasu matasa da ake zargin ƴan IPOB ne suka kashe mutanen biyu sakamakon harin da suka kai musu a Oyigbo.

Ya ce bai san dalilin da yasa suka kai musu harin ba amma yana tunanin ba zai rasa nasaba da barazanar da ƴan kungiyar ta IPOB suka yi wa hausawan mazauna Rivers ba a baya.

Ya yi kira da rundunar ƴan sanda ta yi bincike ta gano wadanda suka kai harin ta kuma hukunta su.

DUBA WANNAN: Sun mayar da mu karuwai, ga horo da yunwa: Yar Najeriya da aka ceto daga Libya

Duk yunkurin da aka yi na tuntubar Kakakin rundunar ƴan sanda na jihar Rivers, SP Nnamdi Omoni a wayar tarho don jin ta bakinsa ya ci tura.

A bangarensa, shugaban ƙaramar hukumar Oyigbo, Prince Gerald Oforji ya yi tir da harin da aka kai wa hausawan inda ya bukaci su zauna lafiya kuma kada su dauki doka a hannun su.

A wani rahoton daban kun ji wasu ƴan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari asibitin koyarwa ta jami'ar Ilorin a ranar Alhamis 3 ga watan Satumba sun sace Sarkin Fulanin Ilorin, Usman Adamu Harɗo.

Ƴan bindigan sun kai harin ne misalin karfe 8 na safe kamar yadda Linda Ikeji ta ruwaito.

Rahotanni sun ce Sarkin Fulanin yana hanyarsa ta zuwa banki ne a cikin mota tare da ɗansa Babangida yayin da wasu ƴan bindigan suka tare motarsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel