Da sana'ar sayar da kifi nake daukar nauyin karatun 'ya'yana a jami'a

Da sana'ar sayar da kifi nake daukar nauyin karatun 'ya'yana a jami'a

- Hanah Miyebi, wata mata mai kokarin gaske, ta bayyana cewa tana amfani da sana'arta ta sayar da kifi wajen daukar nauyin karatun 'ya'yanta

- Matar ta bayyana cewa tana samun kudi sosai da wannan sana'ar kafin annobar coronavirus ta kunno kai ta kawo mata tsaiko wajen cinikin da take yi

- A cewarta, bata taba karbar wani taimako daga wajen gwamnati ba ta kowacce hanya tun lokacin da ta fara sana'arta

Akwai 'yan Najeriya da yawan gaske, da ba wai iya kokari ne da su ba kawai, suna kuma samun kudi sosai da rayuwa mai kyau da sana'ar da suke yi.

Wata mata mai suna Hanah Miyebi daga Gbaramatu a wata hira da tayi da Legit TV ta bayyana yadda take amfani da sana'arta ta sayar da kifi wajen daukar nauyin karatun 'ya'yanta a jami'a.

Da sana'ar sayar da kifi nake daukar nauyin karatun 'ya'yana a jami'a
Da sana'ar sayar da kifi nake daukar nauyin karatun 'ya'yana a jami'a
Asali: Original

Da sana'arta ta sayar da soyayye da gasashen kifi, matar tace tana sayar da jaka daya ta kifi akan kudi naira dubu ashirin, (N20,000), inda tace tana samun kudi mai yawan gaske a wannan sana'ar ta. Hanah ta kara da cewa tana sayar da jaka ashirin a rana.

Da aka tambayeta ko ta taba samun wani tallafi daga wajen gwamnati, ta ce a'a. Ta kara da cewa ita bata taba koda wasa cika takardar neman tallafi ba, saboda ta san cewa gwamnati bata fiya cika alkawuran da take dauka ba.

KU KARANTA: Saurayi ya sassara budurwarsa a kan zarginta da asirin tsotse masa mazakuta

Matar ta bayyana cewa tana zuwa kasuwa da misalin karfe 7:30 zuwa 8:00 na safe a kowacce rana, sannan kuma ta bar kasuwarda karfe 6 na yamma.

Da take bayani akan yadda dokar hana fita ta shafi kasuwancinta, Hannah ta ce ta samu raguwar ciniki sosai, saboda rufe iyakokin jihohi da aka yi a Najeriya.

Matar ta ce da yawa daga cikin masu sayen kifi a wajenta basu dawo mata da kudadenta ba, saboda haka ya sanya take rokon gwamnatin tarayya da ta cire dokar hana fita ta kyale kowa yayi rayuwa yadda ya kamata.

Ta kara da cewa 'ya'yanta suna wurare daban-daban a Najeriya, inda wasu daga cikinsu ma tuni sunyi aure. Matar ta kara da cewa yanzu shekarar ta 32 tana wannan sana'a.

KU KARANTA: Gwamnan PDP ya tube rawanin sarkinsa, bayan ya ziyarci Buhari, ya maye gurbinsa

Haka kuma, Legit.ng ta kawo muku labarin wani dalibin aji daya a jami'a mai suna Jimoh John Yakubu, ya dauki sana'arshi da matukar muhimmanci, inda ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar 9 ga watan Agusta.

Yakubu ya ce sana'ar koko ita ce hanyar samun abincin shi, kuma da ita yake amfani wajen biyan bukatunshi da kuma biyawa kanshi kudin makaranta.

Dan kasuwar mai shekaru 21 dan asalin jihar Ado Ekiti ya kara da cewa yana yin kokon launi daban-daban, sannan ya bashi dandano daban-daban.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel