'Yadda muka kashe wasu masu jego, kuma muka yi awon gaba da jariransu'

'Yadda muka kashe wasu masu jego, kuma muka yi awon gaba da jariransu'

- Rundunar 'yan sanda ta cafke wasu gawurtattun masu safarar yara da ke kashe masu jego suna yin awon gaba da jaririnsu

- Masu safarar, Mary Ishamel (68) tare da abokin aikinta, Chinedu Nwachukwu (23), su ne rundunar ta cafke da aikata wannan laifi

- Dangane da rawar da ta taka wajen sace jariran, Ishamel ta ce bata da masaniya kan hakan, amma Nwachukwu ya ce lallai ita ce ta kitsa masa komai

Rundunar 'yan sanda ta cafke wasu gawurtattun masu safarar yara a jihar Rivers, wadanda suka labarta yadda suka kashe wata mai jego tare da awon gaba da jaririnta.

Bayan sace jaririn, kungiyar masu safarar, sun labarta yadda suka sayar da shi, da kuma raba kudin a tsakaninsu, kafin dubun su ta cika, aka cafke su.

Masu safarar, Mary Ishamel (68) tare da abokin aikinta, Chinedu Nwachukwu (23), na daga cikin mutane 15 da rundunar 'yan sandan jihar Rivers ta yi holensu ga manema labarai.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Joseph Mukan, a Fatakwal, babban birnin jihar Rivers, ya ce an cafke Nwachukwu a shingen binciken rundunar na Omerelu Nipping, kusa da Owerri, jihar Imo.

A cewarsa, tawagar 48 PMF na rundunar 'yan sandan ne suka tsare motar 'yan ta'addan don gudanar da bincike, inda suka same su da jariri dan watanni 5 da haihuwa.

KARANTA WANNAN: Buhari zai kaddamar da shirin tallafawa 'yan kasuwa da N50,000 a kowanne wata

'Yadda muka kashe wasu masu jego, kuma muka yi awon gaba da jariransu'
'Yadda muka kashe wasu masu jego, kuma muka yi awon gaba da jariransu'
Source: Twitter

Da farko an ajiye Nwachukwu a ofishin rundunar na Elele, kafin aka mayar da shi sashen binciken 'yan ta'adda, tare da jaririn, inda ya fallasa yadda suka kashe uwar yaron.

Ya shaida masu cewa, sun sace jaririn bayan kashe mahaifiyarsa, inda suka jefar da gawarta a wani kango a garin Igwuruta, karamar hukumar Ikwerre da ke cikin jihar.

Ana kuma zargin mutanen biyu da bacewar wata mai jego a yankin da shi Nwachukwu ya ke zama, mai suna Chinonye Queen Uzoma tare da jaririyarta yar watanni uku da haihuwa.

A cewar rundunar 'yan sandan, Nwachukwu ya amsa laifinsa da kashe Uzoma, tare da yin awon gaba da jaririyarta, inda ya sayarwa Ishamel akan N250,000.

Ita kuma Ishmael, ta sayar da jaririn akan N350,000 ga wani mutum mazaunin garin Benin, jihar Edo.

KARANTA WANNAN: Fargabar kawo hari: An tsaurara matakan tsaro a Abuja da kewaye

A nata bangaren, Mary Ishamel ta shaidawa rundunar 'yan sandan cewa: "Ina aiki a matsayin unguwar zoma a wani asibiti. Ina da kuma shaguna na kaina, ni sananna ce a unguwarmu.

"Shi Chinedu (Nwachukwu) ne ya same ni, ya sanar da ni budurwarsa ta haihu amma ta gudu. Ya ce bashi da karfin rainon jaririn, don haka yana son bayar da ita ga wadanda zasu iya kula da ita, in har za a biya shi.

"Ya tabbatar mun cewa babu matsala a cikin lamarin, cewar mahaifiyar jaririn ta san da maganar kyautar da yarinyar.

"Da farko ban amince ba, amma ya matsa mun. To dama akwai wasu a Benin da suka taba tuntuba ta kan suna neman yaran da za su raine su.

"Na kira matar na sanar da ita an samu jaririn. Ta zo da kanta, na bata akan kudi N350,000, a ciki ne ni kuma na ba Chinedu N250,000."

Da aka tambayeta rawar da ta taka wajen sace jariran, ta ce bata da masaniya kan hakan. Amma Nwachukwu ya kafe kan lallai ita ce ta kitsa masa komai, lamarin da ya ja aka kama shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel