FG ba za ta iya cigaba da kashe N5bn a kowanne wata ba a kan 'yan gudun hijira - Majalisa

FG ba za ta iya cigaba da kashe N5bn a kowanne wata ba a kan 'yan gudun hijira - Majalisa

Kwamitin ayyuka na musamman na majalisar dattawan Najeriya, ta ce gwamnatin tarayya na kashe naira biliyan biyar a kowanne wata a kan 'yan gudun hijira da ke yankin arewa maso gabas.

An kafa sansanonin 'yan gudun hijira a yankin saboda tsanantar al'amuran mayakan ta'addancin Boko Haram.

Ana ci gaba da rasa rayuka tare da kadarori sakamakon yadda mayakan ta'addancin suka addabi yankin, jaridar The Cable ta wallafa.

A yayin zantawa da manema labarai a ranakun karshen mako, Yusuf Yusuf, shugaban kwamitin, ya ce gwamnati ba za ta iya ci gaba da kashe wannan makuden kudaden ba a kan 'yan gudun hijira.

Sanatan ya ce dole ne kowanne mataki na gwamnati ya tabbatar da dawowar 'yan gudun hijira zuwa yankunansu.

"Na ga abun takaici da alhini a sansanin 'yan gudun hijira. Akwai mutane 2.7 miliyan a sansanin 'yan gudun hijirar da ke jihohin arewa maso gabas. Babu yawan kudin da za a kashe wanda zai ishesu," yace.

FG ba za ta iya cigaba da kashe N5bn a kowanne wata ba a kan 'yan gudun hijira - Majalisa
FG ba za ta iya cigaba da kashe N5bn a kowanne wata ba a kan 'yan gudun hijira - Majalisa. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sojoji sun cafke 'yan bindiga 4 da miyagun makamai, sun ragargaza sansaninsu a Benue

"Gwamnati da abokanan cigabanta na yin iyakar kokarinsu wurin ganin 'yan gudun hijirar sun rayu. Ba za mu iya ci gaba da kashe naira biliyan biyar a kowanne wata ba domin kula da 'yan gudun hijirar.

"Ba za mu amince wannan al'amarin yaci gaba ba. Dole ne mu kawo dakilewarsa a yanzu.

"Abinda ya kamata dukkanmu mu yi shine aiki tare. Mu yadda cewa tsaro yana da matukar amfani. A bai wa jami'an tsaron isassun kayan aiki domin ganin sauyi.

"Jama'ar da ke zama a sansanin gudun hijira duk su koma gida. Babu dalilin da zai hana su komawa," yace.

A wani labari na daban, gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da shirinta na fara bai wa kauyukan arewa maso gabas agaji ta hanyar cilla wa 'yan gudun hijira abinci ta sama.

Ministan kula da walwala da jin kan 'yan kasa, Sadiya Farouk, ta shaida wa 'yan jarida a Maiduguri.

A ranar Lahadi ta sanar da cewa za a fara yin amfani da jiragen sojin saman Najeriya domin wurga kayayyakin tallafi kamar su bargo da abinci.

Ta sanar da cewa akwai manyan matsalolin da suke fuskanta na kai wa ga jama'ar da ke cikin kauyuka. Hakan yasa tace za su fara cilla kayan ta jiragen sama ga kauyukan da motoci basu iya zuwa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel