Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai yi tafiya waje gobe

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai yi tafiya waje gobe

Shugaba Muhammadu Buhari zai shilla kasar Nijar ranar Litinin domin halartan taron shugabannin kasan yankin Afrika ta yamma karkashin gammayar ECOWAS.

Mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, ya bayyana hakan ranar Lahadi, a shafinsa na Tuwita.

Ya ce Buhari zai samu rakiyar manyan ministocinsa kuma zai dawo bayan zaman.

Garba Shehu yace: "Shugaba Muhammadu Buhari zai tashi daga Abuja zuwa Niamey, jamhurriyar Nijar domin halartan taron gangamin shugabannin kasar yankin Afrika ta yamma ECOWAS karo na 57.

"A taron da za'ayi cikin kwana daya, za'a tattauna kan rahoto na musamman kan COVID-19 da shugaba Buhari zai gabatar bayan nadashi zakaran yaki da COVID-19 a taron yanar gizon da akayi ranar 23 ga afrilu, 2020."

"Hakazalika za'a tattauna kan lamarin ta'addanci, barandanci da kuma juyin mulkin da Sojoji sukayi a kasar Mali."

"Bayan haka, za'a tattauna kan zabukan yan majalisa da shugaban kasa da zasu gudana shekaran nan a Burkina Faso, Cote d'ivoire, Ghana da Nijar."

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai yi tafiya waje gobe
Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai yi tafiya waje gobe
Asali: Depositphotos

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel