A kan tsaro: Fitaccen Malami ya zazzagi Buhari, ya ce bashi da amfani (Bidiyo)

A kan tsaro: Fitaccen Malami ya zazzagi Buhari, ya ce bashi da amfani (Bidiyo)

Sannanen abu ne idan aka ce matsalar tsaro ta ki ci balle cinyewa a arewacin Najeriya. Da farko mayakan ta'addancin Boko Haram sun addabi yankin arewa maso gabas, amma yanzu 'yan bindiga sun gangaro yankin arewa ta yamma da ta tsakiya.

Wannan matsalar ta kasance tana ci wa jama'a da dama tuwo a kwarya.

Sheik Adam Albani fitaccen malami ne wanda lamarin ya matukar saka shi cikin damuwa.

Wani bidyonsa da ya bayyana yana yi wa shugaban kasa Buhari 'wankin babban bargo' ya janyo cece-kuce.

A cikin bidiyon wanda ya fara da sautin murya amma daga bisani ya kare da hoto, ya bayyana cewa Shugaba Buhari bashi da amfani kwata-kwata.

Ya yi fatan kada Allah ya sake gwadawa 'yan Najeriya mulki irin wannan wanda ke cike da tashin hankali.

Ya bukaci gwamnati da ta tashi tsaye wurin bai wa rayukan jama'a da dukiyoyinsu kariya, domin kuwa hakan yana daga cikin hakkin jama'a a kan gwamnatin.

Ga bidiyon a kasa:

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel