Sojoji sun cafke 'yan bindiga 418 da masu hako ma'adanai 315

Sojoji sun cafke 'yan bindiga 418 da masu hako ma'adanai 315

Dakarun rundunar Operation Sahel Sanity ta damke 'yan bindiga 418 da wasu masu hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba har 315 a yankin arewa maso yamma.

Kakakin shugaban fannin yada labarai na rundunar, Birgediya janar Bernard Onyeuko, ya bayyana hakan a matsayin nasarorin da rundunar ta samu a jihar Katsina a ranar Asabar.

Onyeuko ya yi bayanin cewa, rundunar Operation Sahel Sanity sun samo bindigogi kirar AK 47 har guda 43, bindigogin toka 100, harsasai 3,261 da wasu 151 a cikin jihohi Katsina, Sokoto, Zamfara, Kaduna da Neja.

Ya ce daga watan Yuli zuwa yanzu, rundunar ta samu nasarar halaka 'yan bindiga 100, masu kai musu bayanai 20 sai masu samar musu da makamai shida.

Kamar yadda yace, a wannan lokacin an ragargaza sansanin 'yan bindigar har 81 sannan an halaka fitattun shugabannin 'yan bindigar.

Sojoji sun cafke 'yan bindiga 418 da masu hako ma'adanai 315
Sojoji sun cafke 'yan bindiga 418 da masu hako ma'adanai 315. Hoto daga Daily Trust
Source: UGC

KU KARANTA: Matar aure ta cafke mazakutar mijinta da hakora, ta bar shi rai sama-sama

Oneyuko ya sanar da cewa, an samu kwato shanu 3,984, tumaki 1,627 da akuyoyi tare da rakuma, Vanguard ta ruwaito.

Ya ce an mika dabbobin ga hukumomin da suka dace wadanda za su mayar wa da masu shi hannunsu.

Onyeuko ya tabbatarwa da yankunan da lamarin ya shafa cewa, rundunar sojin ta shirya ganin bayan duk wani nau'in ta'addancin da ya addabesu.

Ya yi kira ga mazauna yankin da su gaggauta sanar da jami'an tsaro duk wani abu da suka zarga ba na gaskiya bane a yankin.

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jiihar Katsina a yammacin Alhamis sun cafke 'yan bindiga fiye da 50 tare da kwato shanun sata 220 a kashi na biyun kokarinsu na yakar 'yan bindiga, fashi da makami, satar shanu, garkuwa da mutane da wasu nau''in laifuka a jihar.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Sanusi Buba Sanusi, ya sanar da manema labarai a wata tattaunawa da suka yi a hedkwatarsu a Katsina cewa, rundunar ta samo bindigogi kirar AK 47 guda 9, bindigar toka 20, ababen hawa biyu da babura 20.

Ya ce, "A tsawon lokacin nan, rundunar 'yan sandan sun yi ayyukansu a wurare daban-daban kuma sun yi nasarar kamo 'yan bindigar da suka addabi jihar Katsina."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel