Karin mutum 162 sun kamu da cutar korona a Najeriya, jimilla 54,905

Karin mutum 162 sun kamu da cutar korona a Najeriya, jimilla 54,905

Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 162 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:25 na daren ranar Asabar 5 ga Satumba shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 162 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka:

Karin mutum 162 sun kamu da cutar korona a Najeriya
Karin mutum 162 sun kamu da cutar korona a Najeriya
Asali: Facebook

Lagos-53

Gombe-21

Oyo-19

Delta-12

Ondo-11

Plateau-10

Ebonyi-9

DUBA WANNAN: Sun mayar da mu karuwai, ga horo da yunwa: Yar Najeriya da aka ceto daga Libya

FCT-6

Kwara-6

Kaduna-5

Rivers-3

Ogun-2

Anambra-2

Imo-2

Ekiti-1

Jimillar wadanda suka kamu - 54,905

Jimillar wadanda suka warke - 42,922

Jimillar wadanda cutar ta kashe - 1,054

A wani labarin daban, kun ji ministan Ilimi na ƙasar Faransa, Jean-Michel Blanquer, a ranar Juma'a ya tabbatar da rufe makarantu 22 saboda ƙaruwar cutar coronavirus.

Mista Blanquer ya ce fiye da rabin sabbin wadanda suka kamu da cutar sun fito ne daga La Reunion.

Da ya ke zanta wa da gidan rediyon Europa 1, ya ce ya gamsu da yadda lamura ke tafiya tun bayan da dalibai suka koma makaranta ranar Talata.

An rufe makarantu 10 a cikin birnin Faransa yayin da sauran 12 kuma daga wani yanki ne na La Reunion inda ake samun sabbin wadanda suka kamu.

An dakatar da ajujuwa kimanin 130 a makarantun kuma ministan ya ce mahukunta suna bincike a kan sabbin mutum kimanin 250 da ke kamuwa da cutar ta sanadin makarantu a kullum.

Mutanen suna kamuwa da cutar ne daga wasu mutanen a wajen makaranta da ya yi wu sun kamu tun watanni da suka gabata.

A kan rufe makarantun idan an samu fiye da mutum uku da suka kamu da ƙwayar cutar ta Covid-19.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel