Boko Haram na shirin kai hari Abuja, Kogi da Nasarawa - Gwamnatin tarayya

Boko Haram na shirin kai hari Abuja, Kogi da Nasarawa - Gwamnatin tarayya

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa yan ta'addan Boko Haram na shirin kai farmaki babbar birnin tarayya Abuja, da jihohin da ke makwabtaka.

Gwamnatin ta ce yan ta'addan na shirin kai hari ne wasu wurare na musamman a birnin tarayya kuma tuni sun kafa mabuya guda biyar a Abuja.

A cewar wata takardar da Kontrollan hukumar hana fasa kwabri wato kwastam, H.A Sabo, ya saki ranar 20 ga Agusta, 2020, ya bukaci dukkan hafsoshin su kasance cikin farga, Sahara Reporter ta ruwaito.

Boko Haram na shirin kai gari Abuja, Kogi da Nasarawa - Gwamnatin tarayya
Boko Haram na shirin kai gari Abuja, Kogi da Nasarawa - Gwamnatin tarayya
Source: Twitter

Takardar tace: "Labarin da Kontrola Janar na hukumar Kwastam ya samu ya nuna cewa akwai mabuyan yan ta'addan Boko Haram a ciki da wajen birnin tarayya Abuja."

"Karin bayani ya nuna cewa suna shirin kai hari wasu wurare cikin birnin."

"An samu rahoton cewa sun kafa sansani a wuraren nan; Dajin Kunyam, hanyar tashar jirgin sama Abuja, Dajin Rubochi/Gwagwalada, Dajin Kuje Abuja, Dajin Unaisha a karamar hukumar Toto na jihar Nasarawa, Gegu, kusa da garin Idu a jihar Kogi."

"Saboda haka, ana sanar da ku kasance cikin tsaro a koda yaushe. Ku tabbatar labarin nan ya yadu."

Za ku tuna cewa harin farko da aka taba kaiwa Abuja ranar 1 ga Oktoba, 2010, yan watanni bayan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

A bangare guda, Hukumar Sojin Najeriya ta yi shelar cewa jami'an atisayen Operation Sahel Sanity da aka tura Katsina da wasu jihohin Arewa maso yammacin Najeriya sun karya lagon yan bindigan da hare-harensu daga watan Yuli zuwa yanzu.

Mukaddashin diraktan labaran hedkwatar tsaro, Birgediya Janar Benard Onyeuko, ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai a sansanin Soji dake Faskari, jihar Katsina.

Yace: "Atisayen Operation Sahel Sanity da aka tura domin taimakawa Operation Hadarin Daji sun samu nasarar karya lagon hare-haren da yan bindiga ke kaiwa."

"Babu tantama mun kawo karshen halin rashin tsaro da ya hana mutane zuwa gonaki da ayyukan kasuwancinsu a wannan yanki."

"Kawo yanzu a dukkan farmakin da aka kai, an kashe yan bindiga 100, an kwato shanu 3,984, tumakai 1,627 da rakuma 3, kuma an damke yan bindgia 148 da masu satan ma'adinai 315."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel