Zamu tura jami'ai 30,000 don tabbatar da tsaro a zaben jihar Ondo- Hukumar yan sanda

Zamu tura jami'ai 30,000 don tabbatar da tsaro a zaben jihar Ondo- Hukumar yan sanda

- Hukumar yan sanda za ta tura jami'anta 30,000 lokacin zaben gwamnan jihar Ondo

- INEC za ta gudanar da zaben gwamnan jihar ranar Asabar, 10 ga Oktoba

- Kwamishanan yan sandan jihar, Bolaji Salami, ya bayyana hakan a Akura, birnin jihar

Hukumar yan sandan Najeriya ta bayyana cewa za ta tura akalla jami'ai 30,000 jihar Ondo domin tabbatar da tsaro a zaben gwamnan jihar da zai gudana ranar 10 ga Oktoba.

Vanguard ta ruwaito cewa kwamishanan yan sandan jihar, Bolaji Salami, wanda ya bayyana hakan a Akure, birnin jihar, ya ce ba za'a hana yan kasashen waje shiga jihar lokacin zaben ba.

"Hedkwatar hukumar yan sanda ta tura jami'ai 30,000 dukkan kananan hukumomi 18 dake jihar."

"Insfekta Janar na yan sanda ya bada umurnin cewa a tura yan sanda hudu kowani rumfar zabe domin bayar da tsaro."

"An yi hakan ne domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron masu zabe a jihar."

"Hakazalika an shirya samun taimako daga sauran hukumomin tsaro." A cewarsa

Kwamishanan ya bayyana cewa ba za a lamunci sayan kuri'u ba, kuma sauran hukumomi da ma'aikatan INEC zasu tabbatar da hakan.

Ya kara da cewa yan sanda zasu kasance a kowani rumfar zabe tun ana saura kwana uku zaben.

Zamu tura jami'ai 30,000 don tabbatar da tsaro a zaben jihar Ondo- Hukumar yan sanda
Zamu tura jami'ai 30,000 don tabbatar da tsaro a zaben jihar Ondo- Hukumar yan sanda
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Online view pixel