Mun gama da yan bindigan jihar Katsina - Hukumar Sojin Najeriya ta yi shela

Mun gama da yan bindigan jihar Katsina - Hukumar Sojin Najeriya ta yi shela

Hukumar Sojin Najeriya ta yi shelar cewa jami'an atisayen Operation Sahel Sanity da aka tura Katsina da wasu jihohin Arewa maso yammacin Najeriya sun karya lagon yan bindigan da hare-harensu daga watan Yuli zuwa yanzu.

Mukaddashin diraktan labaran hedkwatar tsaro, Birgediya Janar Benard Onyeuko, ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai a sansanin Soji dake Faskari, jihar Katsina.

Yace: "Atisayen Operation Sahel Sanity da aka tura domin taimakawa Operation Hadarin Daji sun samu nasarar karya lagon hare-haren da yan bindiga ke kaiwa."

"Babu tantama mun kawo karshen halin rashin tsaro da ya hana mutane zuwa gonaki da ayyukan kasuwancinsu a wannan yanki."

"Kawo yanzu a dukkan farmakin da aka kai, an kashe yan bindiga 100, an kwato shanu 3,984, tumakai 1,627 da rakuma 3, kuma an damke yan bindgia 148 da masu satan ma'adinai 315."

"Mun kwato manyan makamai da harsasai wanda ya hada da bindigogin AK47 guda 43, GPMG 1, kananan bindigogi 100, harsasai 7.62mm 3,261 da carbin harsasai 151."

"A dukkan binciken da muka gudanar, an ceto mutanen da aka sace 107, an damke masu kaiwa yan bindigan labarai 20, masu kai musu makamai 6, masu sayan shanun sata 13 da kuma masu kaiwa yan bindigan kayayyaki 32."

Ya kara da cewa an ragargaza mabuyar yan bindiga 81, yayinda aka kawar da hare-haren yan bindiga 74 da kokarin garkuwa da mutane 54.

Ya jinjinawa jaruman Sojojin bisa jajircewansu wajen kawar da yan bindiga a Arewa maso yamma kuma ya yi kira ga al'umma su taimakawa Soji da bayanai.

Mun gama da yan bindigan jihar Katsina - Hukumar Sojin Najeriya ta yi shela
Mun gama da yan bindigan jihar Katsina - Hukumar Sojin Najeriya ta yi shela
Asali: Twitter

A bangare guda, Jami'an Sojoji da yan sanda sun kawar da wasu yan bindiga da suka budewa matafiya wuta a hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Juma'a, 4 ga watan Satumba, 2020.

Daily Trust ta tattaro cewa babu wanda ya mutu amma wasu matafiya da jami'an tsaro sun jikkata kuma ana kula da su.

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce jami'an tsaro sun samu nasarar kawar da yan bindigan.

Sun bude wutan ne kusa da kamfanin abincin kaji na Olam.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel