Allura ta tono garma: Fasto ya kashe Boka

Allura ta tono garma: Fasto ya kashe Boka

Hukumar yan sanda a jihar Anambara ta ce an kaddamar da bincike domin gano gaskiyar lamari gaba da kisan Bokan da ake zargi wani Fasto da shi.

A wani takardar da aka saki ranar Juma'a a Awka, babbar birnin jihar Anambara, kakakin hukumar yan sandan jihar, Haruna Mohammed, ya ce Bokan da aka kashe, Oliver Ugwu, na da shekaru 60 a duniya kuma mazaunin kauyen Umusiome ne a Nkpor, kusa da Onitsha.

Ya ce Faston, Uchenna Chukwuma, wanda mazaunin titin Ugwuezue ne a unguwar ya kashe Bokan ta hanyar sara da adda ranar 3 ga Satumba, 2020.

"Mai laifin, wanda asalin dan garin Amagunze ne a karamar hukumar Nkanu ta gabas ya bayyanawa yan sanda yayin bincike cewa Ubangijinsa ne ya umurceshi ya kashe bokan," Kakakin yan sanda ya bayyana.

"Ya kara da cewa Bokan na damunsa a ruhance kuma ya hana shi samun nasara a rayuwa da arziki a duniya."

Haruna yace jami'an yan sandan dake ofishin Ogidi karkashin DPO Ekuri Remiguis sun ziyarci idan abin ya faru kuma suka garzaya da bokan asibitin Iyi Enu.

Ya ce yayinda aka isa asibitin Likita ya tabbatar da cewa ya mutu kuma aka ajiye gawarsa a dakin ajiye gawawwaki domin bincike.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel